ZAB 18

Waƙar Dawuda ta Nasara

1 Ina ƙaunarka ƙwarai, ya Ubangiji!

Kai ne mai kāre ni.

2 Ubangiji ne Mai Cetona,

Shi ne garkuwata mai ƙarfi.

Allahna, shi ne yake kiyaye ni,

Lafiya nake sa’ad da nake tare da shi,

Yana kiyaye ni kamar garkuwa,

Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.

3 Na yi kira ga Ubangiji,

Yakan cece ni daga magabtana,

Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

4 Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,

Halaka ta auko mini a kai a kai.

5 Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,

Kabari kuma ya ɗana mini tarko.

6 A shan wahalata na kira ga Ubangiji,

Na yi kira ga Allahna domin neman taimako.

A Haikalinsa ya ji muryata,

Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

7 Sai duniya ta raurawa ta girgiza,

Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgiza

Saboda Allah ya husata!

8 Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa,

Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.

9 Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,

Tare da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.

10 Ya sauko ta bisa bayan kerubobi,

Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.

11 Ya rufe kansa da duhu,

Gizagizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi.

12 Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko

Daga cikin walƙiya da take gabansa,

Suka keto ta cikin gizagizai masu duhu.

13 Sa’an nan Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama,

Aka ji muryar Maɗaukaki.

Ƙanƙara da garwashin wuta suka sauko.

14 Ya harba kibansa, ya watsa magabtana,

Da walƙatawar walƙiya ya kore su.

15 Kashiyar teku ta bayyana,

Tussan duniya sun bayyana,

Sa’ad da ka tsauta wa magabtana, ya Ubangiji,

Sa’ad da kuma ka yi musu tsawa da fushi.

16 Ubangiji ya miƙa hannunsa daga samaniya ya ɗauke ni,

Ya tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi.

17 Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi,

Daga kuma dukan masu ƙina,

Gama sun fi ƙarfina!

18 Sa’ad da nake shan wahala suka auka mini,

Amma Ubangiji ya kiyaye ni.

19 Ya fisshe ni daga cikin hatsari,

Ya cece ni, don yana jin daɗina.

20 Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne,

Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.

21 Na yi biyayya da umarnan Ubangiji,

Ban yi wa Ubangiji Allahna tawaye ba.

22 Na kiyaye dukan dokokinsa,

Ban yi rashin biyayya da umarnansa ba.

23 Ya sani ba ni da laifi,

Domin na kiyaye kaina daga mugunta.

24 Don haka ya sāka mini, domin ni adali ne,

Gama ya sani ni marar laifi ne.

25 Kai, ya Ubangiji, mai aminci ne ga masu aminci,

Kai nagari ne, cikakke ga kamilai.

26 Kai Mai Tsarki ne ga waɗanda suke tsarkaka,

Amma kana gāba da mugaye.

27 Kakan ceci masu tawali’u,

Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.

28 Ubangiji yakan ba ni haske,

Allah yakan kawar da duhuna.

29 Yakan ba ni ƙarfin da zan fāɗa wa magabtana,

Da ikon rinjayar kagararsu.

30 Wannan Allah dai! Ayyukansa kamiltattu ne ƙwarai,

Maganarsa abar dogara ce!

Kamar garkuwa yake, ga duk mai neman taimako a wurinsa.

31 Ubangiji shi kaɗai ne Allah,

Allah ne kaɗai kāriyamu.

32 Shi ne Allahn da yake ƙarfafa ni,

Yana kiyaye lafiyata a kan hanya.

33 Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa.

Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.

34 Yakan horar da ni don yaƙi,

Domin in iya amfani da baka mafi ƙarfi.

35 Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni,

Na zama babban mutum saboda kana lura da ni,

Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.

36 Ka tsare ni, ba a kama ni ba,

Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.

37 Na kori magabtana, har na kama su,

Ba zan tsaya ba, sai na yi nasara da su.

38 Zan buge su har ƙasa, ba kuwa za su tashi ba,

Za su fāɗi ƙarƙashin ƙafafuna.

39 Kakan ba ni ƙarfin yin yaƙi,

Kakan ba ni nasara a kan magabtana.

40 Ka kori magabtana daga gare ni,

Zan hallaka waɗanda suke ƙina.

41 Suna kukan neman taimako, amma ba wanda zai iya cetonsu,

Za su yi kira ga Ubangiji, amma ba zai amsa ba.

42 Zan murƙushe su har su zama ƙura

Wadda iska take kwashewa,

Zan tattake su kamar caɓi a titi.

43 Ka cece ni daga mutane masu tawaye,

Ka naɗa ni in yi mulkin sauran al’umma,

Jama’ar da ban san ta ba, ta zama abin mulkina.

44 Za su yi biyayya sa’ad da suka ji ni,

Baƙi za su rusuna mini,

45 Za su karai,

Su fita, suna rawar jiki daga kagaransu.

46 Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai kāre ni!

Allah ne, Mai Cetona! A yi shelar girmansa!

47 Yakan ba ni nasara a kan magabtana,

Yakan sa jama’a a ƙarƙashina,

48 Yakan cece ni daga maƙiyana.

Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji,

Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,

49 Don haka zan yabe ka a cikin al’ummai,

Zan raira maka yabo.

50 Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara.

Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa,

Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.