Addu’ar Neman Tsare Mutunci
1 Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji,
Gama na yi abin da suke daidai,
Na dogara gare ka gaba ɗaya.
2 Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji,
Ka gwada muradina da tunanina.
3 Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni,
Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.
4 Ba na tarayya da mutanen banza,
Ba abin da ya gama ni da masu riya.
5 Ina ƙin tarayya da masu mugunta,
Nakan kauce wa mugaye.
6 Ya Ubangiji, na wanke hannuwana
Don in nuna ba ni da laifi,
Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.
7 Na raira waƙar godiya,
Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.
8 Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake,
Inda ɗaukakarka yake zaune.
9 Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi,
Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,
10 Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci,
A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.
11 Amma ni, ina yin abin da yake daidai,
Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!
12 Na kuɓuta daga dukan hatsarori,
A taron sujada na yabi Ubangiji!