Ubangiji Ne Haskena da Cetona
1 Ubangiji ne haskena da cetona,
Ba zan ji tsoron kowa ba.
Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari,
Ba zan ji tsoro ba.
2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini,
Suna ƙoƙari su kashe ni,
Za su yi tuntuɓe su fāɗi.
3 Ko da rundunar mayaƙa ta kewaye ni,
Ba zan ji tsoro ba.
Ko da magabtana sun tasar mini,
Zan dogara ga Allah.
4 Abu guda nake roƙo a wurin Ubangiji,
Abu ɗaya kaɗai nake bukata,
Shi ne in zauna a masujadar Ubangiji,
In yi ta al’ajabin alherinsa
Dukan kwanakin raina,
In roƙi biyarwarsa a can.
5 A lokatan wahala zai kiyaye ni a inuwarsa,
Zai kiyaye ni lafiya a Haikalinsa,
Zai ɗora ni a kan dutse mai tsayi, ya kiyaye ni.
6 Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni.
Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa!
Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji!
7 Ka ji ni, ya Ubangiji, sa’ad da na ya yi kira gare ka!
Ka yi mini jinƙai ka amsa mini!
8 Ka ce, “Zo wurina,”
Zan kuwa zo gare ka, ya Ubangiji,
9 Kada ka ɓoye mini fuskarka, ya Ubangiji!
Kada ka yi fushi da ni,
Kada kuwa ka kori bawanka.
Kai ne kake taimakona, tun dā ma,
Kada ka bar ni, kada ka yashe ni,
Ya Allahna, Mai Cetona!
10 Mai yiwuwa ne ubana da uwata su yashe ni,
Amma Ubangiji zai lura da ni.
11 Ka koya mini abin da ya kamata in yi, ya Ubangiji,
Ka bi da ni kan lafiyyiyar hanya,
Domin ina da magabta da yawa.
12 Kada ka bar ni a hannun magabtana,
Waɗanda suke fāɗa mini da ƙarairayi da kurari.
13 Hakika zan rayu domin in ga alherin Ubangiji
Da zai yi wa jama’arsa.
14 Ka dogara ga Ubangiji!
Ka yi imani, kada ka karai.
Ka dogara ga Ubangiji!