Addu’ar Godiya domin Kuɓuta daga Mutuwa
1 Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni,
Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.
2 Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna,
Ka kuwa warƙar da ni.
3 Ka dawo da ni daga lahira.
Na gangara tare da waɗanda suke gangarawa cikin zurfafa a ƙasa,
Amma ka ceci raina.
4 Ku raira yabo ga Ubangiji,
Ku amintattun jama’arsa!
Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata,
Ku yi masa godiya!
5 Fushinsa ba ya daɗewa,
Alherinsa kuwa har matuƙa ne.
Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare,
Amma a yi murna da safe.
6 Ina zaune jalisan, na ce wa kaina,
“Faufau ba za a taɓa cin nasara a kaina ba.”
7 Kana yi mini alheri, ya Ubangiji,
Ka kiyaye ni kamar a kagarar dutse.
Amma sa’ad da ka ɓoye mini fuskarka,
Sai in cika da tsoro.
8 Ina kira gare ka, ya Ubangiji,
Ina roƙon taimakonka.
9 Wane amfani za a samu daga mutuwata?
Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari?
Ko matattu suna iya yabonka?
Za su iya shelar madawwamin alherinka?
10 Ka ji ni, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!
Ka taimake ni, ya Ubangiji!
11 Ka mai da baƙin cikina
Ya zama rawar farin ciki,
Ka tuɓe mini tufafin makoki,
Ka sa mini na farin ciki.
12 Don haka ba zan yi shiru ba,
Zan raira maka yabo,
Ya Ubangiji, kai ne Allahna,
Zan gode maka har abada.