Kewar Allah a Baƙuwar Ƙasa
1 Kamar yadda kishimi yake marmarin ruwan sanyi daga rafi,
Haka nake marmarinka, ya Allah.
2 Ina jin ƙishinka, ya Allah, ya Allah Mai Rai,
Yaushe zan tafi in yi sujada a gabanka?
3 Dare da rana ina kuka,
Hawayena kaɗai su ne abincina,
A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata,
“Ina Allahnka?”
4 Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce,
Sa’ad da nakan tafi tare da taron jama’a zuwa Haikalin Allah,
Ina bishe su a jere.
Taron jama’a masu farin ciki, suna raira waƙa,
Suna ta da murya, suna yabon Allah.
5 Me ya sa nake baƙin ciki haka?
Me ya sa nake damuwa ƙwarai?
Zan dogara ga Allah,
Zan sāke yin yabonsa,
Mai Cetona, Allahna.
6 Zuciyata ta karai
Saboda haka zan tuna da kai
A wajen Urdun, da kusa da Dutsen Harmon, da na Mizar,
Zan tuna da kai.
7 Zurfafan tekuna suna kiran junansu,
Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri!
Igiyoyin ruwa na baƙin ciki
Suka yi wa raina ambaliya.
8 Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana!
Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare,
In yi addu’a ga Allah, wanda ya ba ni rai.
9 Ga Allah wanda yake tsarona na ce,
“Me ya sa ka manta da ni?
Me ya sa nake ta shan wahala
Saboda muguntar maƙiyana?”
10 An ragargaza ni da zargin maƙiyana
Waɗanda suke tambayata kullum,
“Ina Allahnka?”
11 Me ya sa ni ɓacin rai haka?
Me ya sa ni damuwa?
Zan dogara ga Allah.
Har yanzu ma zan yabe shi,
Mai Cetona, Allahna.