Addu’ar Neman Ceto
1 Da kunnuwanmu muka ji, ya Allah,
Kakanninmu suka faɗa mana,
Manya manyan abubuwa da ka aikata a lokacinsu,
A zamanin dā,
2 Yadda kai da kanka ka kori arna,
Ka dasa jama’arka a ƙasarsu,
Yadda ka hori sauran al’umma,
Amma ka sa jama’arka su wadata.
3 Ba da takubansu suka ci ƙasar ba,
Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba,
Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka,
Ta wurin tabbatar musu kana tare da su,
Kana nuna musu kana ƙaunarsu.
4 “Ya Allah, kai ne Sarkina,
Ka ba jama’arka nasara.
5 Da ikonka muka kori abokan gābanmu,
Saboda kasancewarka tare da mu
Muka rinjayi magabtanmu.
6 Ban dogara ga bakana ba,
Takobina kuwa ba zai cece ni ba.
7 Amma ka cece mu daga abokan gābanmu,
Ka kori waɗanda suke ƙinmu.
8 Za mu yabe ka kullum,
Mu yi maka godiya har abada.”
9 Amma yanzu, ya Allah, ka yashe mu,
Ka bari aka kore mu,
Ba ka ƙara fita ka yi tafiya tare da sojojinmu ba.
10 Ka sa muka gudu daga gaban abokan gābanmu,
Suka ƙwace abin da muke da shi.
11 Ka bari aka yanyanka mu kamar tumaki,
Ka warwatsar da mu a baƙuwar ƙasa.
12 Ka sayar da jama’arka
A bakin ‘yan kuɗi ƙalilan,
Ba ka ci ribar cinikin ba.
13 Maƙwabtanmu suna yi mana dariya saboda kai,
Suna yi mana ba’a, sun maishe mu abin wasa.
14 Ka maishe mu abin raini a wurin arna,
Suna kaɗa mana kai, suna raina mu.
15 Kullum a cikin kunya nake,
Kunya ta lulluɓe ni ɗungum,
16 Saboda dukan wulakanci,
Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.
17 Dukan wannan ya same mu,
Ko da yake ba mu manta da kai ba,
Ba mu kuma ta da alkawarin da ka yi da mu ba.
18 Ba mu ci amanarka ba,
Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.
19 Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan,
Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.
20 Da a ce mun daina yin sujada ga Allahnmu,
Muka yi addu’a ga gumaka,
21 Hakika ka gane,
Domin ka san asirin tunanin mutane.
22 Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci,
Ake kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka.
23 Ka tashi, ya Ubangiji! Me ya sa kake zama kamar mai barci?
Ka tashi! Kada ka yashe mu har abada!
24 Me ya sa ka ɓuya mana?
Kada ka manta da ƙuncinmu da wahalarmu!
25 Mun fāɗi, an turmushe mu a ƙasa,
An bar mu kwance cikin ƙura.
26 Ka tashi ka taimake mu!
Ka fanshe mu saboda madawwamiyar ƙaunarka!