Addu’ar Neman Tsari daga Mugaye
1 Ka kasa kunne ga kalmomina, ya Ubangiji,
Ka kuma ji ajiyar zuciyata.
2 Ya Sarkina, Allahna,
Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.
3 A gare ka zan yi addu’a, ya Ubangiji,
Da safe za ka ji muryata,
Da hantsi zan yi addu’ata,
In kuma jira amsa.
4 Kai ba Allah mai yarda da aikin kuskure ba ne,
Ba ka yarda da mugunta a gabanka.
5 Ba ka jurewa da ganin mutane masu fāriya,
Kana ƙin mugaye.
6 Kakan hallakar da duk maƙaryata,
Kakan raina masu ta da hankali da masu ruɗi.
7 Amma ni, ina iya zuwa wurinka,
Saboda ƙaunarka mai girma,
In yi sujada a tsattsarkan Haikalinka,
In kuma rusuna maka da bangirma.
8 Ina da abokan gāba da yawa, ya Ubangiji,
Ka bi da ni in aikata nufinka,
Ka kuma fayyace mini hanyarka domin in bi ta!
9 Abin da maƙiyana ke faɗa,
Ba abin da za a yarda da shi ba ne,
Su dai, so suke su hallakar kawai,
Bakinsu kamar buɗaɗɗen kabari yake,
Maganganunsu kuwa suna da taushi da kuma yaudara.
10 Ka kāshe su, ka hukunta su, ya Allah
Ka watsar da mugayen shirye-shiryensu,
Ka kore su daga gabanka sabili da yawan zunubansu,
Da kuma tayarwar da suke yi maka.
11 Duk waɗanda suka fake gare ka za su yi farin ciki,
Kullum za su yi ta raira waƙa domin murna.
Kana kiyaye waɗanda suke ƙaunarka,
Suna kuwa matuƙar murna saboda kai.
12 Ka sa wa masu yi maka biyayya albarka, ya Ubangiji,
Alherinka yana kāre su kamar gārkuwa.