ZAB 7

Addu’ar Neman a Yi Adalci

1 Ya Ubangiji, Allahna, na sami mafaka a wurinka,

Ka cece ni, ka tserar da ni daga dukan masu fafarata,

2 Idan ba haka ba kuwa, za su ɗauke ni,

Su tafi da ni zuwa wurin da ba wanda zai cece ni,

A can za su yayyage ni kamar zaki.

3 Ya Ubangiji, Allahna, idan na aikata ɗaya daga cikin waɗannan,

Wato idan na yi wa wani laifi,

4 Idan na ci amanar abokina,

Ko kuwa in na gwada wa maƙiyi fin ƙarfi ba dalili,

5 To, bari abokan gābana su fafare ni, su kama ni,

Bari su datse ni har ƙasa, su kuma kashe ni,

Su bar ni ƙasa, matacce!

6 Ka tashi da fushinka, ya Ubangiji,

Ka kuma tashi ka yi gāba da hasalar abokan gābana!

Ka tashi, ka taimake ni, gama adalci kake so a yi.

7 Ka tattaro dukan kabilun da suke kewaye da kai,

Ka yi mulki a kansu daga Sama.

8 Ya Ubangiji, kai ne alƙalin dukan mutane.

Ka shara’anta mini bisa ga adalcina,

Gama ba ni da laifi, ina kuma da kirki.

9 Ka tsai da muguntar mugaye,

Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki.

Kai Allah mai adalci ne,

Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.

10 Allah ne mai kiyaye ni,

Yakan ceci waɗanda suke yi masa biyayya.

11 Allah alƙali ne mai adalci,

Kullum kuwa yana kā da mugaye.

12 Idan mutane ba su tuba ba,

Allah zai wasa takobinsa,

13 Zai ɗana bakansa ya shirya shi,

Zai ɗauki makamansa masu dafi,

Ya kuma auna kibansa masu wuta.

14 Ka duba, yadda mugu yake tunanin mugunta a ransa,

Yana shisshirya wahala, yana kuma aikata ruɗi.

15 Yana haƙa rami mai zurfi a ƙasa,

Sa’an nan yă fāɗa ramin da ya haƙa!

16 Saboda haka muguntarsa ta hukunta shi ke nan,

Rikicin kansa ya yi masa lahani.

17 Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa,

Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki.