1 Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.
2 Sa’ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha’awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.
3 Ubangiji yana ganin abin da yake faruwa a ko’ina, yana lura da mu, ko muna aikata alheri ko mugunta.
4 Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun ƙiyayya suna karya zuciyar mutum.
5 Wauta ce mutum ya ƙi kulawa da abin da mahaifinsa ya koya masa, amma hikima ce idan ka karɓi tsautawarsa.
6 Adalai suna adana dukiyarsu, amma mugaye sukan rasa tasu dukiya sa’ad da wahala ta zo.
7 Mutane masu hikima suke yaɗa ilimi, amma banda wawaye.
8 Ubangiji yana murna sa’ad da adalai suke yin addu’a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.
9 Ubangiji yana ƙin hanyoyin mugaye, amma yana ƙaunar mutumin da yake yin abin da yake daidai.
10 Idan ka yi abin da ba daidai ba, za ka sha hukunci sosai, za ka mutu idan ka ƙi yarda da tsautawa.
11 Ko lahira ba za ta hana Ubangiji ya san abin da yake can ba. Ƙaƙa fa mutum zai iya ɓoye wa Allah tunaninsa?
12 Mai girmankai ba ya so a tsauta masa. Faufau ba zai nemi shawara a wurin masu hikima ba.
13 Sa’ad da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa’ad da yake baƙin ciki yakan yi nadama.
14 Mutum mai basira yana neman ilimi, amma dakikai, jahilcinsu ya wadace su.
15 Wahaltaccen mutum a ko yaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.
16 Gara a zauna da talauci da tsoron Ubangiji, da a sami dukiya game da wahala.
17 Gara cin mabunƙusa tare da waɗanda kake ƙauna, da ka ci abinci mai romo a inda ƙiyayya take.
18 Zafin rai yakan kawo jayayya, amma haƙuri yana kawo salama.
19 Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko’ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba.
20 Ɗa mai hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa, amma wawa yana raina mahaifiyarsa.
21 Dakikai suna murna da wautarsu, amma mai hikima zai aikata abin da yake daidai.
22 Ka nemi dukan shawarwarin da ka iya ka samu, za ka yi nasara, idan ba tare da shawara ba, za ka fāɗi.
23 Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!
24 Mutum mai hikima yakan kama hanya ya haura zuwa rai, ba ya bin hanyar da ta gangara zuwa mutuwa.
25 Ubangiji zai rushe gidajen masu girmankai, amma zai kiyaye dukiyar gwauruwa, wato mata wadda mijinta ya mutu.
26 Ubangiji yana ƙin tunanin mugaye, amma yana murna da kalmomi masu daɗi.
27 Mai ƙoƙarin cin ƙazamar riba yana jefa iyalinsa a wahala ke nan. Kada ka karɓi hanci, za ka yi tsawon rai.
28 Mutanen kirki sukan yi tunani kafin su ba da amsa. Mugaye suna da saurin ba da amsa, amma takan jawo wahala.
29 Sa’ad da mutanen kirki sukan yi addu’a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.
30 Fuska mai fara’a takan sa ka yi murna, labari mai daɗi kuma yakan sa ka ji daɗi.
31 Idan ka mai da hakali sa’ad da ake tsauta maka kai mai hikima ne.
32 Idan ka ƙi koyo kana cutar kanka, idan ka karɓi tsautawa za ka zama mai hikima.
33 Tsoron Ubangiji koyarwa ce domin samun hikima. Sai ka zama mai tawali’u kafin ka sami girmamawa.