1 Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.
2 Ka yi gaskiya, za ka nuna girmamawarka ga Ubangiji, amma idan ka yi rashin gaskiya, ka nuna rashin girmamawa ke nan ga Ubangiji.
3 Kalmomin mai hikima za su kiyaye shi, amma maganganun wawa za su jawo masa hukunci.
4 Idan ba ka da shanun noma ba za ka sami hatsi mai yawa ba, amma idan kana da su za ka sami hatsi mai yawan gaske.
5 Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.
6 Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.
7 Ka nisanci wawaye, gama ba su da abin da za su koya maka.
8 Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.
9 Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara.
10 Ɓacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba.
11 Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum.
12 Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.
13 Dariyar mutum takan ɓoye baƙin cikinsa. Sa’ad da murna ta tafi, ko yaushe baƙin ciki yana nan.
14 Mugu zai sami abin da ya cancance shi, mutumin kirki kuma zai sami sakayyar ayyukansa.
15 Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la’akari yana lura da takawarsa.
16 Mutum mai hankali yana lura don ya kauce wa wahala, amma wawa rashin kula gare shi, yakan aikata kome da gaggawa.
17 Mutum mai zafin rai yakan yi aikin wauta, mai mugayen dabaru kuma abin ƙi ne.
18 Jahilai sukan sami abin da ya cancanci wautarsu, amma ilimi shi ne sakamakon masu azanci.
19 Tilas mugaye su rusuna wa adalai, su roƙe su tagomashi da tawali’u.
20 Ba wanda yake son matalauci, amma attajiri yana da abokai da yawa.
21 Idan kana so ka zama mai farin ciki, sai ka nuna alheri ga matalauci. Zunubi ne ka raina kowane mutum.
22 Waɗansu za su amince da kai, su girmama ka, idan ka aikata nagarta, idan kuwa ka aikata mugunta, to, ka yi babban kuskure.
23 Idan ka yi aiki za ka sami abin masarufi, idan kuwa ka zauna kana ta surutu kawai za ka zama matalauci.
24 Mutane masu hikima za a sāka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa.
25 Sa’ad da mashaidi ya faɗi gaskiya zai ceci rayuka, amma maƙaryacin mashaidi yakan ci amanar mutane sa’ad da ya faɗi ƙarairayi.
26 Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa.
27 Kana so ka kauce wa mutuwa? To, tsoron Ubangiji shi ne maɓuɓɓugar rai.
28 Darajar sarki ta dogara ga irin yawan mutane da ya mallaka, idan ba su, shi ba kome ba ne.
29 Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.
30 Kwanciyar rai lafiya ce ga jiki, amma kishi yana kama da ciwon da yake cin ƙashi.
31 Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.
32 Muguntar mugun takan kawo hallakarsa, amma adalin mutum, an kiyaye shi ta wurin dattakonsa.
33 Hikima tana cikin kowane tunani na haziƙi, wawa bai san kome game da hikima ba.
34 Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi yakan kunyatar da al’umma.
35 Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun ‘yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.