1 Ubangiji yana ƙin masu yin awo da ma’aunin zamba, amma yana farin ciki da masu yin awo da ma’auni na gaskiya.
2 Masu girmankai za a kunyatar da su nan da nan. Hikima ce mutum ya zama mai kamewa.
3 Mutanen kirki su ne gaskiya takan bi da su. Rashin aminci kuwa yana hallaka maciya amana.
4 Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.
5 Gaskiya takan sa zaman mutanen kirki ya zama a sawwaƙe, amma mugun mutum shi yake kā da kansa da kansa.
6 Adalci yakan ceci amintaccen mutum, amma marar aminci, haɗamarsa ce take zamar masa tarko.
7 Mugun mutum yakan mutu da burinsa. Dogara ga dukiya bai amfana kome ba.
8 Akan kiyaye adali daga wahala, amma takan auko wa mugu.
9 Mutane sukan sha hasara ta wurin maganar marasa tsoron Allah, amma hikimar adalai takan yi ceto.
10 Birni yakan yi farin ciki saboda wadatar mutanen kirki, akwai kuma sowa ta farin ciki sa’ad da mugaye suka mutu.
11 Biranen da adalai suke cikinsu sukan ƙasaita, amma maganganun mugaye sukan hallakar da su.
12 Wauta ce a yi wa waɗansu maganar raini, amma mutum mai la’akari yakan kame bakinsa.
13 Ba wanda zai yarda ya faɗi asirinsa ga matsegunci, amma za ka amince wa amintaccen mutum.
14 Al’ummar da ba ta da masu ja mata gora, za ta fāɗi. Yawan mashawarta yake kawo zaman lafiya.
15 Wanda ya ɗaukar wa baƙo lamuni zai yi da na sani, zai fi maka sauƙi idan ba ruwanka.
16 Mace mai mutunci abar girmamawa ce, amma azzalumai za su sami dukiya.
17 In ka yi alheri, kanka ka samar wa tagomashi, in kuwa ka yi mugunta, kanka ka cutar.
18 A ainihi mugaye ba su cin ribar kome, amma idan ka yi abin da yake daidai, ka tabbata za a sāka maka da alheri.
19 Mutumin da ya yi niyyar aikata abin da yake daidai zai rayu, amma mutumin da ya dukufa ga aikata mugunta zai mutu.
20 Ubangiji yana ƙin masu muguwar niyya, amma yana murna da waɗanda suke aikata abin da yake daidai!
21 Ka tabbata fa za a hukunta mugaye, amma ba za a hukunta adalai ba.
22 Kome kyan mace idan ba ta da kangado, tana kamar zoben zinariya a hancin alade.
23 Abin da mutanen kirki suke so kullum yakan jawo alheri, idan mugaye sun sami biyan bukatarsu kowa zai yi ɓacin rai.
24 Waɗansu mutane sukan kashe kuɗinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai ƙaruwa yake yi. Waɗansu kuwa saboda yawan tsumulmularsu sukan talauce.
25 Ka yi alheri za ka arzuta. Ka taimaki waɗansu, su kuma za su taimake ka.
26 Mutane sukan la’anci mai ɓoye hatsi, yana jira ya yi tsada, amma sukan yabi wanda yake sayar da nasa.
27 Idan nufe-nufenka na kirki ne za a girmama ka, amma idan kai mai neman tashin hankali ne, to, abin da zai same ka ke nan.
28 Adalai za su arzuta, kamar ganyaye da bazara, amma waɗanda suke dogara ga dukiyarsu za su karkaɗe kamar ganyaye da kaka.
29 Mutumin da yake jawo wa iyalinsa wahala, ƙarshensa talaucewa. Wawaye za su zama barorin masu hikima a ko yaushe.
30 Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.
31 Idan an sāka wa mutumin kirki da alheri a duniya, hakika za a hukunta wa mugaye da masu zunubi.