Faɗakarwa a kan Ragwanci da Ƙarya
1 Ɗana, ka taɓa yin alkawari ka ɗaukar wa wani lamuni?
2 Maganganunka sun taɓa kama ka, ko alkawaranka sun taɓa zamar maka tarko?
3 To, ɗana, kana cikin ikon wannan mutum, amma ga yadda za ka yi ka fita, sheƙa zuwa wurinsa, ka roƙe shi ya sake ka.
4 Kada ka yarda ka yi barci ko ka huta.
5 Ka fita daga cikin tarkon kamar tsuntsu ko barewar da ta tsere wa maharbi.
6 Bari ragwaye su yi koyi da tururuwa.
7 Ba su da shugaba, ba su da sarki, ko mai mulki,
8 amma da kaka sukan tanada wa kansu abinci, domin kwanakin bazara.
9 Har yaushe rago zai yi ta ɓalɓalcewa? Yaushe zai farka?
10 Yakan ce, “Bari in ɗan ruruma, in naɗa hannuwana in shaƙata.”
11 Amma lokacin da yake sharar barci, tsiya za ta auka masa kamar ɗan fashi da makamai.
12 Sakarkari, wato mugaye sukan yi ta baza jita-jita.
13 Sukan yi ƙyifce, ko su yi nuni don su yaudare ka.
14 A kowane lokaci suna shirya mugunta a kangararren hankalinsu, suna kuta tashin hankali ko’ina.
15 Saboda wannan masifa za ta fāɗa musu farat ɗaya ba makawa, za a yi musu mummunan raini.
16-19 Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba,
duban raini,
harshe mai faɗar ƙarya,
hannuwan da suke kashe marasa laifi,
kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru,
mutum mai gaggawar aikata mugunta,
mai yawan shaidar zur,
mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.
Faɗakarwa a kan Zina
20 Ɗana, ka yi abin da mahaifinka ya faɗa maka, kada ka manta da koyarwar mahaifiyarka.
21 Kullum ka kiyaye abin da suke faɗa maka, ka kulle su kuma a zuciyarka.
22 Koyarwarsu za ta bi da kai sa’ad da kake tafiya, ta kiyaye ka da dare, ta kuma ba ka shawara da rana.
23 Doka da abubuwan da take koyarwa haske ne mai haskakawa. Tsautawa tana iya koya maka zaman duniya.
24 Za ta tsare ka daga mugayen mata, daga kalmomin alfasha da suke fitowa daga bakin matan waɗansu.
25 Kada kyansu ya jarabce ka, kada ka faɗa cikin tarkon feleƙensu.
26 Mutum ta dalilin karuwa zai sha hasarar abin da ya mallaka duka ta wurin zina.
27 Ka iya rungumar wuta a ƙirjinka sa’an nan ka ce ba za ta ƙone tufafinka ba?
28 Ka iya tafiya a kan garwashi sa’an nan ka ce ƙafafunka ba za su ƙone ba?
29 Haka yake da mutumin da ya kwana da matar wani. Duk wanda ya aikata wannan, zai sha wahala.
30 Mutane ba sukan raina wanda ya saci abinci don yana jin yunwa ba,
31 duk da haka in an kama shi, sai ya biya diyya sau bakwai, tilas kuwa ya ba da dukan abin da yake da shi.
32 Amma mazinaci marar hankali ne, gama hallaka kansa yake yi.
33 Zai sha dūka, a wulakanta shi, zai dawwama cikin kunya.
34 Hasalar miji mai kishi babu irinta, ramawarsa ba dama.
35 Ba zai karɓi biya ba, ba kyautar da za a yi masa wadda za ta kwantar da fushinsa.