Fa’idodin Hikima
1 ‘Ya’yana ku kasa kunne ga koyarwar mahaifinku. Ku mai da hankali, za ku zama haziƙai.
2 Abin da nake koya muku, abu mai kyau ne, saboda haka ku tuna da shi duka.
3 Sa’ad da nake ɗan yaro tilo a wurin iyayena,
4 mahaifina yakan koya mini, yakan ce, “Ka tuna da abin da nake faɗa maka, kada ka manta. Ka yi abin da na faɗa maka za ka rayu.
5 Ka nemi hikima da basira! Kada ka manta ko ka ƙyale abin da na faɗa.
6 Kada ka rabu da hikima, gama za ta kiyaye ka, ka ƙaunace ta, za ta kiyaye lafiyarka.
7 Samun hikima shi ne mafificin abin da za ka yi. Kome za ka samu dai, ka sami basira.
8 Ka ƙaunaci hikima, za ta girmama ka. Ka rungume ta, za ta kawo maka daraja.
9 Za ta zamar maka rawanin daraja.”
10 Ɗana, ka kasa kunne gare ni. Ka ɗauki abin da nake faɗa maka, muhimmin abu ne, za ka yi tsawon rai.
11 Gama na koya maka hikima da hanyar zama mai kyau.
12 Idan ka yi tafiya da hikima ba abin da zai tsare maka hanya, sa’ad da kake gudu ba za ka yi tuntuɓe ba.
13 Kullum ka tuna da abin da ka koya, iliminka shi ne ranka, ka lura da shi da kyau.
14 Kada ka tafi inda mugaye suke tafiya, kada ka bi gurbin mugaye.
15 Kada ka yi mugunta! Ka nisance ta! Ka ƙi ta, yi tafiyarka.
16 Mugaye ba su iya yin barci, sai sun aikata ɓarna. Ba su barci sai sun cuci wani.
17 Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su.
18 Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka.
19 Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare. Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba.
20 Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa. Ka kasa kunne ga kalmomina.
21 Kada ka kuskura su rabu da kai, ka tuna da su, ka ƙaunace su.
22 Za su ba da rai da lafiya ga dukan wanda ya fahimce su.
23 Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.
24 Kada ka faɗi kowane abu da yake ba na gaskiya ba, kada wani abu ya haɗa ka da ƙarya, ko maganganun ruɗawa.
25 Ka duba gaba sosai gabanka gaɗi, ba tsoro.
26 Ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai.
27 Ka rabu da mugunta ka yi tafiyarka sosai, kada ka kauce ko da taki ɗaya daga hanyar da take daidai.