Sakamakon Neman Hikima
1 Ɗana, ka koyi abin da nake koya maka, sam kada ka manta da abin da na faɗa maka ka yi.
2 Ka kasa kunne ga abin da yake na hikima, ka yi ƙoƙari ka fahimce shi.
3 I, ka roƙi ilimi da tsinkaya.
4 Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya.
5 Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah.
6 Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa.
7 Shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci.
8 Yakan kiyaye waɗanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.
9 Idan ka kasa kunne gare ni za ka san abin da yake daidai, da abin da yake gaskiya, da abin da yake na kirki. Za ka san abin da za ka yi.
10 Za ka zama mai hikima, iliminka zai faranta maka rai.
11 Tsinkayarka da fahiminka za su tsare ka.
12 Za su hana ka aikata mugayen ayyuka, za su nisantar da kai daga mutane masu ta da hargitsi da irin maganganunsu,
13 mutane waɗanda suka bar zaman adalci don su zauna cikin duhun zunubi,
14 waɗanda suke jin daɗin yin laifi, suna nishaɗi cikin mugunta.
15 Ba za a dogara da su ba, ba kuwa za a iya amincewa da su ba.
16 Za a nisantar da kai daga mazinaciya, wadda take ƙoƙari ta lalatar da kai da daɗin bakinta,
17 marar aminci ga mijinta, wadda ta manta da tsarkakan alkawaran da ta ɗauka.
18 Idan ka tafi gidanta ka kama hanyar mutuwa. Tafiya can kama hanyar zuwa lahira ne.
19 Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa. Ba zai ƙara komowa ga hanyar rai ba.
20 Saboda haka dole ka bi hanyar da mutanen kirki suka bi, ka bi gurbin adalai.
21 Mutane adalai, masu kamewa, su ne za su zauna ƙasarmu.
22 Amma Allah zai fizge mugaye daga ƙasar, ya kuma tumɓuke masu zunubi kamar yadda ake tumɓuke shuke-shuke daga ƙasa.