Bari dukan Halittar Allah su yi Yabonsa
1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
Ku yabi Ubangiji daga sama,
Ku da kuke zaune a tuddan sama.
2 Ku yabe shi dukanku mala’ikunsa,
Ku yabe shi, ku dukan rundunansa na sama!
3 Ku yabe shi, ku rana da wata,
Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!
4 Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi duka!
Ku yabe shi, ku ruwayen da kuke bisa sararin sama!
5 Bari su duka su yabi sunan Ubangiji!
Ya umarta, sai suka kasance.
6 Ta wurin umarninsa aka kafa su
A wurarensu har abada,
Ba su kuwa da ikon ƙi.
7 Ku yabi Ubangiji daga duniya,
Ku yabi Ubangiji, ku dodanin ruwa da dukan zurfafan teku.
8 Ku yabe shi, ku walƙiya, da ƙanƙara, da dusar ƙanƙara,
Da gizagizai, da ƙarfafan iska waɗanda suke biyayya da umarnansa!
9 Ku yabe shi, ku tuddai da duwatsu,
Da itatuwa ‘ya’ya da kurama.
10 Ku yabe shi dukanku dabbobi, na gida da na jeji,
Masu rarrafe da tsuntsaye!
11 Ku yabe shi, ku sarakuna da dukan kabilai,
Ku yabe shi, ku shugabanni da dukan hukumomi.
12 Ku yabe shi ku samari da ‘yan mata!
Ku yabe shi, ku tsoffafi da yara!
13 Bari dukansu su yabi sunan Ubangiji,
Sunansa ya fi dukan sauran sunaye girma,
Ɗaukakarsa kuwa tana bisa duniya da samaniya!
14 Ya sa al’ummarsa ta yi ƙarfi,
Domin dukan jama’arsa su yabe shi
Jama’arsa Isra’ila, wadda yake ƙauna ƙwarai!
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!