Addu’ar Neman Ceto da Wadata
1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, mai kiyaye ni,
Ya hore ni don yaƙi,
Ya kuwa shirya ni don yaƙi.
2 Shi yake kiyaye ni,
Shi yake kāre ni,
Shi ne mafakata da Mai Cetona,
Wanda nake dogara gare shi
Don samun zaman lafiya.
Shi ne ya ɗora ni a kan al’ummai.
3 Ya Ubangiji wane ne mutum, har da kake lura da shi?
Wane ne ɗan adam kurum, har da kake kulawa da shi?
4 Shi kamar hucin iska yake,
Kwanakinsa kuwa kamar inuwa mai wucewa ne.
5 Ya Ubangiji, ka kware sararin sama, ka sauko,
Ka taɓa duwatsu, don su tuƙaƙo da hayaƙi.
6 Ka aiko da walƙiyar tsawa ta warwatsa maƙiyanka,
Ka harba kibanka, ka sa su sheƙa a guje!
7 Ka sunkuyo daga Sama,
Ka tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi, ka cece ni,
Ka cece ni daga ikon baƙi,
8 Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,
Sukan yi rantsuwar ƙarya.
9 Zan raira maka sabuwar waƙa, ya Allah,
Zan kaɗa garaya in raira maka waƙa.
10 Ka ba sarakuna nasara,
Ka kuma ceci bawanka Dawuda.
11 Ka cece ni daga mugayen abokan gābana,
Ka ƙwato ni daga ikon baƙi,
Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,
Sukan yi rantsuwar ƙarya.
12 Ka sa ‘ya’yanmu maza waɗanda suke cikin samartaka,
Su zama kamar itatuwan da yake girma da ƙarfi.
Ka sa ‘ya’yanmu mata
Su zama kamar al’amudai,
Waɗanda suke adanta kusurwoyin fāda.
13 Ka sa rumbunanmu su cika
Da kowane irin amfanin gona.
Ka sa tumakin da suke cikin saurukanmu
Su hayayyafa dubu dubu har sau goma,
14 Ka sa shanunmu su hayayyafa,
Kada su yi ɓari ko su ɓace.
Ka sa kada a ji kukan damuwa a kan titunanmu!
15 Mai farin ciki ce al’ummar
Da abin nan da aka faɗa ya zama gaskiya a gare ta.
Masu farin ciki ne jama’ar da Allahnsu shi ne Ubangiji!