Ƙasƙantar Almasihu da kuma Ɗaukakarsa
1 In akwai ƙarfafawa a cikin Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku,
2 to, albarkacinsu ku cikasa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna ƙaunar juna, nufinku ɗaya, ra’ayinku ɗaya.
3 Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali’u, kowa yana mai da ɗan’uwansa ya fi shi.
4 Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan’uwansa ma.
5 Ku ɗauki halin Almasihu Yesu,
6 wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba,
7 sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam.
8 Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye.
9 Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da yake birbishin kowane suna,
10 domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa,
11 kowane harshe kuma yă shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba.
Haskakawa Kamar Fitilu a Duniya
12 Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.
13 Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.
14 Kome za ku yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama,
15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai, ‘ya’yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,
16 kuna riƙe da maganar rai kankan, har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama, cewa himmata da famana ba a banza suke ba.
17 Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.
18 Haka ku ma, ya kamata ku yi farin ciki, ku kuma taya ni farin ciki.
Timoti da Abafaroditas
19 Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timoti da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku.
20 Ba ni da wani kamarsa, wanda da sahihanci zai tsananta kula da zamanku lafiya.
21 Dukansu sha’anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba.
22 Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.
23 Shi ne nake fata in aiko, da zarar na ga yadda al’amarina yake gudana.
24 Na kuma amince har ga Ubangiji, ni ma da kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.
25 Amma na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas ɗan’uwana, abokin aikina, abokin famana kuma, wanda kuka aiko ya yi mini ɗawainiya.
26 Yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya.
27 Lalle ya yi rashin lafiya, har ya yi kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayinsa, ba kuwa shi kaɗai ba, har ni ma, don kada in yi baƙin ciki a kan baƙin ciki.
28 Saboda haka na ɗokanta ƙwarai in turo shi domin ku yi farin cikin sāke ganinsa, ni kuma in rage baƙin cikina.
29 Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane,
30 domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.