Addu’ar Neman Tsari daga Mugaye
1 Ka cece ni daga mugaye, ya Ubangiji,
Ka kiyaye ni daga mutane masu hargitsi.
2 Kullum suna shirya mugunta,
Kullum suna kawo tashin hankali.
3 Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi,
Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.
4 Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji,
Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali,
Waɗanda suke shirya fāɗuwata.
5 Masu girmankai sun kafa mini tarko,
Sun shimfiɗa ragar igiya,
Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.
6 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna.
Ka ji kukana na neman taimako, ya Ubangiji!
7 Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi,
Kā kiyaye ni cikin yaƙi.
8 Ya Ubangiji, kada ka biya wa mugaye burinsu,
Kada ka bar mugayen dabaru su yi nasara!
9 “Kada ka bar maƙiyana su sami nasara,
Ka sa kashedin da suke yi mini yă koma kansu.
10 Ka sa garwashin wuta yă zubo a kansu,
Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.
11 Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace,
Kada su yi nasara.
Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”
12 Na sani kai, ya Ubangiji, kana kāre matsalar talakawa,
Da hakkin matalauta.
13 Hakika adalai za su yabe ka,
Za su zauna a gabanka.