Mutumin da aka Cece shi daga Mutuwa
1 Ina ƙaunar Ubangiji, saboda yana jina,
Yana kasa kunne ga addu’o’ina.
2 Yakan kasa kunne gare ni,
A duk lokacin da na yi kira gare shi.
3 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam,
Razanar kabari ta auka mini,
Na cika da tsoro da alhini.
4 Sa’an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce,
“Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”
5 Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri,
Allahnmu mai rahama ne.
6 Ubangiji yakan kiyaye kāsassu,
Sa’ad da na shiga hatsari ya cece ni.
7 Kada ki yi shakka, ya zuciyata,
Gama Ubangiji yana yi mini alheri.
8 Ubangiji ya cece ni daga mutuwa,
Ya share hawayena,
Bai bari a kāshe ni ba.
9 Don haka nake tafiya a gaban Ubangiji
A duniyar masu rai.
10 Na dai yi ta gaskatawa, ko da yake
Na ce, “An ragargaza ni sarai.”
11 Sa’ad da na ji tsoro na ce,
“Ba wanda za a iya dogara gare shi.”
12 Me zan bayar ga Ubangiji
Saboda dukan alheransa gare ni?
13 Zan miƙa hadaya ta sha ga Ubangiji,
Ina gode masa domin dā ya cece ni.
14 Zan ba shi abin da na alkawarta
A taron dukan jama’arsa.
15 Mutuwar ɗaya daga cikin tsarkakansa,
Abu mai daraja ne!
16 Ni bawanka ne, ya Ubangiji,
Ina bauta maka yadda mahaifiyata ta yi,
Ka ‘yantar da ni.
17 Zan miƙa maka hadaya ta godiya,
Zan yi addu’ata a gare ka.
18-19 A taron dukan jama’arka,
A shirayun Haikalinka,
A Urushalima, zan ba ka abin da na alkawarta.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!