Ubangiji yana Kula da Halittarsa
1 Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Ya Ubangiji Allahna, mai girma ne kai!
Kana saye da ɗaukaka da daraja,
2 Ka yi lulluɓi da haske.
Ka shimfiɗa sammai kamar alfarwa.
3 Ka gina wurin zamanka a bisa kan ruwan da yake sama.
Gajimare ne karusanka,
A bisa kan fikafikan iska kake tafiya.
4 Iska ce jakadanka,
Walƙiya kuwa ita ce baiwarka.
5 Ka sa duniya ta kahu sosai a bisa harsashin gininta,
Ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.
6 Ka sa teku a bisanta kamar alkyabba,
Ruwan kuwa ya rufe manyan duwatsu.
7 Amma sa’ad da ka tsauta wa ruwa,
Sai ya tsere,
Sa’ad da ya ji ka daka tsawa,
Sai ya sheƙa a guje.
8 Ya haura kan duwatsu, ya gangara cikin kwaruruka,
Wurin da ka shirya masa.
9 Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba,
Don kada ya sāke rufe duniya.
10 Ka sa maɓuɓɓugai suka gudano cikin kwaruruka,
Ka sa ruwa yana gudu tsakanin tuddai.
11 Su ne suke shayar da namomin jeji,
Jakunan jeji kuma, a nan sukan kashe ƙishinsu.
12 A itatuwan da suke kusa da wurin,
Tsuntsaye suke yin sheƙunansu suna ta raira waƙa.
13 Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu,
Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.
14 Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu,
Tsire-tsire kuma don amfanin mutum,
Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,
15 Don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki,
Ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara’a,
Da abincin da zai ba shi ƙarfi.
16 Itatuwan al’ul na Lebanon sukan sami isasshen ruwan sama,
Itatuwa ne na Ubangiji kansa, waɗanda shi ya dasa.
17 A nan tsuntsaye suke yin sheƙunansu,
A bisa itatuwan fir shamuwa suke yin sheƙa.
18 A kan duwatsu masu tsayi awakin jeji suke zama,
Remaye sukan ɓuya a kan tsaunukan bakin teku.
19 Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai,
Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.
20 Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.
21 Sagarun zakoki sukan yi ruri sa’ad da suke farauta,
Suna neman abincin da Allah zai ba su.
22 Sa’ad da rana ta fito,
Sai su koma su kwanta a kogwanninsu.
23 Sa’an nan mutane sukan fita su yi aikinsu,
Su yi ta aiki har maraice ya yi.
24 Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa!
Da hikima ƙwarai ka halicce su!
Duniya cike take da talikanka.
25 Ga babbar teku mai fāɗi,
Inda talikai da ba su ƙidayuwa suke zaune,
Manya da ƙanana gaba ɗaya.
26 Jiragen ruwa suna tafiya a kansa,
Dodon ruwa wanda ka halitta, a ciki yake wasa.
27 Dukansu a gare ka suke dogara,
Don ka ba su abinci sa’ad da suke bukata.
28 Ka ba su, sun ci,
Ka tanada musu abinci, sun ƙoshi.
29 Sa’ad da ka rabu da su sukan tsorata,
In ka zare numfashin da ka ba su, sai su mutu,
Su koma turɓaya, da ma da ita aka yi su.
30 Amma sa’ad da ka hura musu numfashi, sai su rayu,
Kakan sabunta fuskar duniya.
31 Da ma darajar Ubangiji ta dawwama har abada!
Da ma Ubangiji ya yi farin ciki da abin da ya halitta!
32 Ya dubi duniya, sai ta girgiza,
Ya taɓa duwatsu, sai suka tuɗaɗo da hayaƙi.
33 Zan raira waƙa ga Ubangiji dukan raina,
Zan raira yabbai ga Allah muddin raina.
34 Da ma ya ji daɗin waƙata,
Saboda yakan sa ni in yi murna.
35 Da ma a hallakar da masu zunubi daga duniya,
Da ma mugaye su ƙare ƙaƙaf!
Ka yabi Ubangiji, ya raina!
Ka yabi Ubangiji!