Alkawarin Sarki domin Zaman Adalci
1 Waƙata ta aminci ce da gaskiya.
Ina raira maka ita, ya Ubangiji.
2 Abin da nake yi ba zai zama laifi ba,
Yaushe za ka zo wurina?
Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.
3 Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan.
Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah,
Ba ruwana da su.
4 Ba zan yi rashin aminci ba,
Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.
5 Zan hallakar da mai raɗar abokinsa,
Ba zan jure da mutum mai girmankai,
Ko mai alfarma ba.
6 Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah,
Zan yardar musu si yi zamansu a fādata,
Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminci
Su yi mini hidima.
7 Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba,
Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba.
8 A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu,
Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji.