Makoki saboda An Lalatar da Urushalima
1 Ya Allah, arna sun fāɗa wa ƙasar jama’arka!
Sun ƙazantar da Haikalinka tsattsarka,
Sun bar Urushalima kufai.
2 Suka bar wa tsuntsaye gawawwakin jama’arka su ci,
Suka bar wa namomin jeji gawawwakin bayinka.
3 Suka zubar da jinin jama’arka kamar ruwa,
Jini ya yi ta gudu kamar ruwa
Ko’ina a Urushalima,
Ba ma wanda ya ragu don yă binne gawawwaki.
4 Sauran al’ummar da take kewaye da mu,
Suka maishe mu abin ba’a, suka yi mana dariya,
Suka yi mana ba’a.
5 Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji?
Har abada ne?
Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
6 Ka yi fushi da al’umman da ba su yi maka sujada,
Ka yi fushi da jama’ar da suka ƙi ka!
7 Sun karkashe mutanenmu,
Sun kuwa lalatar da ƙasarmu.
8 Kada ka hukunta mu saboda zunuban kakanninmu,
Amma ka yi mana jinƙai yanzu,
Gama mun fid da zuciya sarai.
9 Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,
Saboda girmanka.
Ka cece mu, ka gafarta mana zunubanmu,
Don mutane su yabe ka.
10 Don me al’ummai za su tambaye mu cewa,
“Ina Allahnku?”
Bari mu ga ka hukunta al’ummai
Saboda sun zubar da jinin bayinka!
11 Ka kasa kunne ga nishin ‘yan sarƙa,
Ka kuɓutar da waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa,
Ta wurin ikonka mai girma.
12 Ya Ubangiji, ka rama wa al’umman nan har sau bakwai,
Saboda tsiwace-tsiwacen da suka yi maka.
13 Mu waɗanda muke jama’arka, tumakin garkenka,
Za mu gode maka, mu yabe ka har abada.