Ƙarshen Mugaye
1 Hakika, Allah yana yi wa Isra’ila alheri,
Da waɗanda suke da tsarkin zuciya!
2 Amma ina gab da fāɗuwa,
Ƙafafuna sun kusa zamewa,
3 Saboda na ji kishin masu girmankai,
Sa’ad da na ga mugaye suna arziki.
4 Ba su jin zafin ciwo,
Su ƙarfafa ne, lafiyayyu.
5 Ba su shan wahala yadda sauran mutane suke sha,
Ba su da wahala kamar sauran mutane,
6 Don haka suka ɗaura girmankai kamar dutsen wuya,
Suka sa hargitsi kuma kamar riga.
7 Zuciyarsu, cike take da mugunta,
Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle.
8 Sukan yi wa waɗansu ba’a,
Suna faɗar mugayen abubuwa,
Masu girmankai ne su, suna shawara
A kan yadda za su zalunci waɗansu.
9 Sukan faɗi baƙar magana a kan Allah na Sama,
Su ba da umarnai na girmankai ga mutane a duniya,
10 Har jama’ar Allah ma sukan koma wurinsu,
Suna ɗokin gaskata dukan abin da suke faɗa musu.
11 Sukan ce, “Ai, Allah ba zai sani ba,
Maɗaukaki ba zai bincika ba!”
12 Haka mugaye suke.
Suna da dukiya da yawa, amma sai ƙaruwa suke ta yi.
13 Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki,
Hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi?
14 Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini,
Kana horona kowace safiya!
15 Da na faɗi waɗannan abubuwa,
Da na zama marar gaskiya ga jama’arka.
16 Don haka na yi iyakar ƙoƙari in fahimci wannan,
Ko da yake ya cika wuya,
17 Sai sa’ad da na shiga Haikalinka,
Sa’an nan na fahimci abin da zai sami mugaye.
18 Hakika ka sa su a wurare masu santsi,
Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!
19 Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su,
Suka yi mummunan ƙarshe!
20 Ya Ubangiji, kamar mafarki suke
Wanda akan manta da shi da safe,
Sa’ad da mutum ya farka yakan manta da kamanninsa.
21 Sa’ad da zuciyata ta ɓaci,
Hankalina ya tashi,
22 Sai na zama wawa, ban fahimta ba,
Na nuna halin dabba a gabanka.
23 Duk da haka ina tare da kai kullayaumin,
Kana riƙe da hannuna.
24 Shawararka, tana bi da ni,
Daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.
25 In banda kai, wa nake da shi a Sama?
Tun da yake ina da kai, me kuwa nake bukata a duniya?
26 Kwanyata da jikina za su raunana,
Amma Allah ne ƙarfina,
Shi nake so har abada!
27 Hakika waɗanda za su rabu da kai za su mutu,
Za ka hallakar da marasa aminci gare ka.
28 Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah!
Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah,
Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata.