Waƙar Nasara ta Al’ummar Ƙasar
1 Da ma Allah ya tashi ya warwatsa maƙiyansa!
Da ma su waɗanda suke ƙinsa su gudu!
2 Kamar yadda iska take korar hayaƙi,
Haka nan zai kore su,
Kamar yadda kākin zuma yakan narke a gaban wuta,
Haka nan mugaye za su hallaka a gaban Allah.
3 Amma adalai za su yi murna,
Su kuma yi farin ciki a gaban Allah,
Za su yi murna ƙwarai da gaske.
4 Ku raira waƙa ga Allah,
Ku raira waƙar yabo ga sunansa,
Ku yi hanya ga wanda yake ratsa gizagizai.
Sunansa kuwa Ubangiji ne, ku yi murna a gabansa!
5 Allah, wanda yake zaune a tsattsarkan Haikalinsa,
Yana lura da marayu, yana kuwa kiyaye gwauraye,
Wato matan da mazansu suka mutu.
6 Yakan ba waɗanda suke da kewa gida, su zauna a ciki,
Yakan fitar da ‘yan sarƙa ya kai su ‘yanci mai daɗi,
Amma ‘yan tawaye za su zauna a ƙasar da ba kowa a ciki.
7 Sa’ad da ka bi da jama’arka, ya Allah,
Sa’ad da ka yi tafiya a hamada,
8 Duniya ta girgiza, sararin sama ya kwararo ruwa,
Saboda bayyanar Allah, har Dutsen Sinai ya girgiza,
Saboda bayyanar Allah na Isra’ila.
9 Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah,
Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.
10 Jama’arka suka gina gidajensu a can,
Ta wurin alherinka ka yi wa matalauta tanadi.
11 Ubangiji ya ba da umarni,
Sai mata masu yawa suka baza labari cewa,
12 “Sarakuna da rundunan sojojinsu suna gudu!
Matan da suke a gida suka rarraba ganima.”
13 Suna kamar kurciyoyin da aka dalaye da azurfa,
Waɗanda fikafikansu suna ƙyalli kamar kyakkyawar zinariya.
(Me ya sa waɗansunku suke zaune cikin shingen tumaki?)
14 Sa’ad da Allah Mai Iko Dukka
Ya warwatsar da sarakuna a dutsen Zalmon,
Sai ya sa dusar ƙanƙara ta sauka a wurin.
15 Wane irin babban dutse ne wannan dutsen Bashan?
Tulluwarka nawa, dutsen Bashan?
16 Me ya sa, daga manyan kawunanka
Kake yi wa dutsen da Allah ya zaɓa
Ya zauna a kai, duban raini?
A nan Ubangiji zai zauna har abada!
17 Daga Sinai da dubban manyan karusansa,
Ubangiji ya zo tsattsarkan Haikalinsa.
18 Ya hau kan tsaunuka
Tare da ɗumbun waɗanda ya kamo daga yaƙi,
Yana karɓar kyautai daga wurin mutane,
Daga wurin ‘yan tawaye kuma.
Ubangiji Allah zai zauna a can.
19 Ku yabi Ubangiji,
Wanda yake ɗaukar nawayarmu ta yau da kullum,
Shi ne Allah wanda ya cece mu.
20 Allahnmu, Allah Mai Ceto ne,
Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu,
Wanda yake cetonmu daga mutuwa.
21 Hakika Allah zai farfashe kawunan abokan gābansa,
Da na waɗanda suka nace bin hanyoyinsu na zunubi.
22 Ubangiji ya ce, “Zan komo da su daga Bashan,
Zan komo da su daga zurfin teku,
23 Don ku wanke sawayenku a cikin jinin maƙiyanku,
Karnukanku kuwa za su lashe iyakar abin da suke so.”
24 Ya Allah, jama’a duka sun ga irin tafiyarka ta nasara,
Irin tafiyar Allah, Sarkina, zuwa tsattsarkan wurinsa.
25 Mawaƙa suna kan gaba, mabusa suna biye,
A tsakiya kuwa ‘yan mata suna kaɗa bandiri.
26 “Ku jama’ar Allah, ku yabe shi cikin taronku,
Ku yabi Ubangiji, dukanku, ku zuriyar Isra’ila!”
27 Ga Biliyaminu mafi ƙanƙanta
Cikin kabilai, a kan gaba,
Sa’an nan shugabannin Yahuza da ƙungiyarsu,
Daga nan sai shugabannin Zabaluna da na Naftali suna biye da su.
28 Ka nuna ikonka, ya Allah,
Ikon nan da ka nuna saboda mu.
29 Daga Haikalinka a Urushalima,
Sarakuna sukan kawo maka kyautai.
30 Ka tsauta wa Masar, naman jejin nan
Mai zafin hali da yake cikin iwa,
Ka tsauta wa sauran al’umma, taron bijiman nan da ‘yan maruƙansu,
Har dukansu su durƙusa, su miƙa maka azurfarsu.
Ka warwatsar da jama’ar nan
Masu son yin yaƙi!
31 Wakilai za su zo daga Masar,
Habashawa za su miƙa hannuwansu sama,
Su yi addu’a ga Allah.
32 Ku raira waƙa ga Allah, ku mulkokin duniya,
Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,
33 Shi wanda ya hau cikin sararin sama,
Daɗaɗɗen sararin sama!
Ku kasa kunne ga muryarsa mai ƙarfi!
34 Ku yi shelar ikon Allah,
Ɗaukakarsa tana bisa kan Isra’ila,
Ikonsa yana cikin sararin sama.
35 Allah al’ajabi ne a tsattsarkan wurinsa,
Allah na Isra’ila!
Yana ba da ƙarfi da iko ga jama’arsa.
Ku yabi Allah!