Yabo da Miƙa Hadaya ta Godiya
1 Ya Allah, dole mutane su yabe ka a Sihiyona,
Tilas su ba ka abin da suka alkawarta.
2 Saboda kakan amsa addu’o’i,
Dukan mutane za su zo wurinka.
3 Zunubanmu sun kāshe mu,
Amma za ka gafarta zunubanmu.
4 Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe su
Su zauna a tsattsarkan wurinka!
Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka,
Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!
5 Ka amsa mana, ya Allah Mai Cetonmu,
Ka kuma cece mu ta wurin aikata al’amuran banmamaki.
Mutane daga ko’ina a duniya,
Har da waɗanda suke can nesa a hayin tekuna,
Sun dogara gare ka.
6 Ka kakkafa duwatsu ta wurin ikonka,
Ka bayyana ƙarfin ikonka.
7 Kakan kwantar da rurin tekuna,
Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa,
Kakan kwantar da tarzomar jama’a.
8 Dukan duniya ta tsorata,
Saboda manyan ayyuka da ka aikata.
Ayyukanka sukan kawo sowa ta farin ciki
Daga wannan iyakar duniya zuwa wancan.
9 Kakan nuna kana kulawa da ƙasar,
Ta wurin aiko mata da ruwa.
Ka arzuta ta, ta zama dausayi.
Rafuffukan da ka bayar ba su taɓa ƙafewa ba,
Sun sa ƙasar ta ba da amfanin gonaki,
Abubuwan da ka aikata ke nan.
10 Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome,
Ka jiƙe su da ruwa,
Ka tausasa ƙasar da yayyafi,
Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.
11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka!
Inda ka tafi duka akwai wadata!
12 Makiyaya suna cike da tumaki masu ƙiba,
Tuddai kuma suna cike da farin ciki.
13 Sauruka suna cike da tumaki,
Kwaruruka suna cike da alkama,
Suna sowa suna raira waƙa ta farin ciki!