Addu’ar Neman Tsari
1 Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu’ata!
Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana!
2 Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye,
Da iskancin mugayen mutane.
3 Sukan wasa harsunansu kamar takuba,
Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.
4 Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau,
Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro.
5 Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu,
Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu.
“Ba wanda zai gan mu,” in ji su.
6 Sukan shirya maƙarƙashiya, su ce,
“Ai, mun gama shirin aikata laifi sarai.”
Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa!
7 Amma Allah zai harbe su da kibansa,
Za a yi musu rauni nan da nan.
8 Zai hallaka su saboda maganganunsu,
Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa.
9 Dukansu za su ji tsoro,
Za su faɗi abin da Allah ya aikata,
Su yi tunani a kan ayyukansa.
10 Dukan masu adalci za su yi murna,
Saboda abin da Ubangiji ya aikata.
Za su sami mafaka a gare shi,
Dukan mutanen kirki za su yabe shi.