Allah ne kaɗai Mafaka
1 Ga Allah kaɗai na dogara,
Cetona daga gare shi yake fitowa.
2 Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,
Shi ne kariyata,
Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.
3 Har yaushe dukanku za ku fāɗa wa wani don ku yi nasara da shi,
Kamar rusasshen garu,
Ko kuma dangar da ta fāɗi?
4 Ba abin da kuke so, sai ku ƙasƙantar da shi daga maƙaminsa na daraja,
Kuna jin daɗin yin ƙarairayi.
Kuna sa masa albarka,
Amma a zuciyarku la’antarwa kuke yi.
5 Ga Allah kaɗai na dogara,
A gare shi na sa zuciyata.
6 Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,
Shi ne kariyata,
Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.
7 Cetona da darajata daga Allah ne,
Shi ne ƙaƙƙarfan makiyayina,
Shi ne mafakata.
8 Ya jama’ata, ku dogara ya Allah a kowane lokaci!
Ku faɗa masa dukan wahalarku,
Gama shi ne mafakarmu.
9 Talakawa kamar shaƙar numfashi suke,
Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani.
Ko an auna su a ma’auni, sam ba su da nauyin kome,
Sun fi numfashi shakaf.
10 Kada ku dogara da aikin kama-karya.
Kada ku sa zuciya za ku ci ribar kome ta wurin fashi.
In kuwa dukiyarku ta ƙaru,
Kada ku dogara gare ta.
11 Sau ɗaya Allah ya faɗa,
Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.
12 Madawwamiyar ƙauna, ta Ubangiji ce.
Kai kanka, ya Ubangiji, kake sāka wa
Kowane mutum bisa ga ayyukansa.