Addu’ar Roƙon Gafara
1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,
Sabili da madawwamiyar ƙaunarka.
Ka shafe zunubaina,
Saboda jinƙanka mai girma!
2 Ka wanke muguntata sarai,
Ka tsarkake ni daga zunubina!
3 Na gane laifina,
Kullum ina sane da zunubina.
4 Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa,
Na kuwa aikata mugunta a gare ka.
Daidai ne shari’ar da ka yi mini,
Daidai ne ka hukunta ni.
5 Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni,
Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.
6 Amintacciyar zuciya ita kake so,
Ka cika tunanina da hikimarka.
7 Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka,
Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.
8 Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.
Ko da yake ka ragargaza ni,
Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.
9 Ka kawar da fuskarka daga zunubaina,
Ka shafe duk muguntata.
10 Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah,
Ka sa sabon halin biyayya a cikina.
11 Kada ka kore ni daga gabanka,
Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.
12 Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,
Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.
13 Sa’an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka,
Za su kuwa komo wurinka.
14 Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona,
Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.
15 Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji,
Zan kuwa yabe ka.
16 Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,
Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
17 Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah,
Zuciya mai ladabi da biyayya,
Ba za ka ƙi ba, ya Allah.
18 Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta,
Ka sāke gina garun Urushalima.
19 Sa’an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi,
Da dukan hadayun ƙonawa.
Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.