Addu’ar Roƙo da Yabo
1 Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni,
Ka ji kukana!
In kuwa ba ka amsa mini ba,
Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira.
2 Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako,
Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.
3 Kada ka kāshe ni tare da mugaye,
Tare da masu aikata mugunta,
Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce,
Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.
4 Ka hukunta su saboda abin da suka aikata.
Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu,
Ka ba su abin da ya cancance su!
5 Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba,
Ko kuma abin da ya halitta,
Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada.
6 A yabi Ubangiji,
Gama ya ji kukana na neman taimako!
7 Ubangiji yakan kiyaye ni, yă tsare ni.
Na dogara gare shi.
Ya taimake ni, don haka ina murna,
Ina raira masa waƙoƙin yabo.
8 Ubangiji yana kiyaye jama’arsa,
Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi.
9 Ka ceci jama’arka, ya Ubangiji,
Ka sa wa waɗanda suke naka albarka!
Ka zama makiyayinsu,
Ka lura da su har abada.