Addu’a domin Biyarwa, da Gafartawa, da Kiyayewa
1 A gare ka nake yin addu’a, ya Ubangiji,
2 A gare ka nake dogara, ya Allah.
Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa,
Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!
3 Waɗanda suke dogara gare ka,
Ba za su kasa yin nasara ba,
Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.
4 Ka koya mini al’amuranka, ya Ubangiji,
Ka sa su zama sanannu a gare ni.
5 Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka,
Gama kai Mai Cetona ne.
Dukan yini ina dogara a gare ka.
6 Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka,
Waɗanda ka nuna tun a dā.
7 Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata.
Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka,
Ka tuna da ni, ya Ubangiji!
8 Ubangiji mai adalci ne, mai alheri,
Yana koya wa masu zunubi tafarkin da za su bi.
9 Yana bi da masu tawali’u a tafarkin da suke daidai,
Yana koya musu nufinsa.
10 Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa.
11 Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.
12 Waɗanda suke biyayya da Ubangiji
Za su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.
13 Kullayaumi za su arzuta,
‘Ya’yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.
14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi,
Yakan koya musu alkawarinsa.
15 A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako,
Yakan kuɓutar da ni daga hatsari.
16 Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,
Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi.
17 Damuwar zuciyata ta yi yawa,
Ka raba ni da dukan damuwa,
Ka cece ni daga dukan wahalata.
18 Ka kula da wahalata da azabata,
Ka gafarta dukan zunubaina.
19 Ka duba yawan magabtan da nake da su,
Dubi irin ƙiyayyar da suke yi mini!
20 Ka yi mini kāriya, ka cece ni,
Gama na zo wurinka neman kāriya.
21 Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni,
Gama na dogara gare ka.
22 Ka fanshi jama’arka daga dukan wahalarsu, ya Allah!