Kukan Azaba da Waƙar Yabo
1 Ya Allahna, ya Allahna,
Don me ka yashe ni?
Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako,
Amma har yanzu ba ka zo ba!
2 Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna,
Amma ba ka amsa ba.
Da dare kuma na yi kira,
Duk da haka ban sami hutawa ba.
3 Amma an naɗa ka Mai Tsarki,
Wanda Isra’ila suke yabonsa.
4 Kakanninmu suka dogara gare ka,
Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.
5 Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari,
Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.
6 A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai,
Rainanne, abin ba’a ga kowa da kowa!
7 Duk wanda ya gan ni
Sai yă maishe ni abin dariya,
Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.
8 Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji,
Me ya sa bai cece ka ba?
Idan Ubangiji na sonka,
Don me bai taimake ka ba?”
9 Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni,
A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.
10 Tun daga lokacin da aka haife ni nake dogara gare ka,
Kai ne Allahna tun daga ran da aka haife ni.
11 Kada ka yi nisa da ni!
Wahala ta gabato,
Ba kuwa mai taimako.
12 Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai,
Dukansu suna kewaye da ni,
Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.
13 Sun buɗe bakinsu kamar zakoki,
Suna ruri, suna ta bina a guje.
14 Ƙarfina ya ƙare,
Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa.
Dukan gaɓoɓina sun guggulle,
Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.
15 Maƙogwarona ya bushe kamar ƙura,
Harshena kuma na liƙe wa dasashina na sama.
Ka bar ni matacce cikin ƙura.
16 Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni,
Suka taso mini kamar garken karnuka,
Suka soke hannuwana da ƙafafuna.
17 Ana iya ganin ƙasusuwana duka.
Magabtana suka dube ni, suka zura mini ido.
18 Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,
Suka jefa kuri’a a kan babbar rigata.
19 Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!
Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!
20 Ka cece ni daga takobi,
Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.
21 Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki,
Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.
22 Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi,
Zan yabe ka cikin taronsu.
23 “Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji!
Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu!
Ku yi masa sujada, ku jama’ar Isra’ila!
24 Ba ya ƙyale matalauta,
Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu,
Ba ya rabuwa da su,
Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”
25 Zan yabe ka a gaban babban taron jama’a
Saboda abin da ka yi,
A gaban dukan masu yi maka biyayya,
Zan miƙa sadakokin da na alkawarta.
26 Matalauta za su ci yadda suke so,
Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi,
Su arzuta har abada!
27 Dukan al’ummai za su tuna da Ubangiji,
Za su zo gare shi daga ko’ina a duniya,
Dukan kabilai za su yi masa sujada.
28 Ubangiji Sarki ne,
Yana mulki a kan al’ummai.
29 Masu girmankai duka za su rusuna masa,
‘Yan adam duka za su rusuna masa,
Dukan waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa.
30 Zuriya masu zuwa za su bauta masa,
Mutane za su ambaci Ubangiji ga zuriya mai zuwa.
31 Mutanen da ba a haifa ba tukuna, za a faɗa musu,
“Ubangiji ya ceci jama’arsa!”