Mafakar Adalai
1 Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya,
Wauta ce idan kun ce mini,
“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,
2 Domin mugaye sun ja bakkunansu,
Sun kuma ɗana kibansu
Domin su harbi mutanen kirki a duhu.
3 Ba abin da mutumin kirki zai iya yi
Sa’ad da kome ya lalace.”
4 Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa,
Yana da kursiyinsa a Sama.
Yana kallon dukan mutane
Yana sane da abin da suke yi.
5 Yana auna masu kirki da mugaye dukka,
Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.
6 Yakan aukar da garwashin wuta
Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye,
Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna.
7 Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar kyawawan ayyuka,
Masu yi masa biyayya za su zauna a gabansa.