Godiya ga Allah saboda Adalcinsa
1 Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji,
Zan hurta dukan abubuwa masu banmamaki da ka yi.
2 Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai,
Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki!
3 Magabtana sun jā da baya da suka gan ka,
Suka faɗi, suka mutu.
4 Kai da kake alƙali mai adalci
Ka zauna a kursiyinka,
Ka kuwa yi shari’ar da ta yi mini daidai.
5 Ka kā da arna,
Ka kuma hallakar da mugaye,
Ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba.
6 An hallaka abokan gābanmu har abada,
Ka lalatar da biranensu,
An kuma manta da su sarai.
7 Amma Ubangiji sarki ne har abada,
Ya kafa kursiyinsa domin yin shari’a.
8 Yana mulkin duniya da adalci,
Yana yi wa mutane shari’a da gaskiya.
9 Ubangiji mafaka ne ga waɗanda ake zalunta,
Wurin ɓuya a lokatan wahala.
10 Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji,
Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.
11 Ku yabi Ubangiji, shi da yake mulki a Sihiyona!
Ku faɗa wa kowace al’umma abin da ya yi!
12 Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya,
Ba ya mantawa da kukansu,
Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu.
13 Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!
Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini!
Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji,
14 Domin in iya tsayawa a gaban jama’ar Urushalima,
In faɗa musu dukan abin da ya sa nake yabonka.
Zan yi farin ciki saboda ka cece ni.
15 Arna sun haƙa rami sun kuwa fāɗa ciki,
Sun ɗana tarko, ya kuwa kama su.
16 Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari’arsa mai adalci,
Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.
17 Mutuwa ce maƙarar dukan mugaye,
Da dukan waɗanda suke ƙin Allah.
18 Ba kullum ne ake ƙyale masu bukata ba,
Ba za a danne sa zuciyar waɗanda ake zalunta ba har abada.
19 Ka zo, ya Ubangiji! Kada ka bari mutane su gagare ka!
Ka kawo arna a gabanka, ka hukunta su.
20 Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji,
Ka sa su sani su mutane ne kawai.