Ɗaukakar Allah da Martabar Mutum
1 Ya Ubangiji, Ubangijinmu,
An san girmanka ko’ina a dukan duniya.
Yabonka ya kai har sammai,
2 Yara da jarirai suna raira shi,
Ka gina kagara saboda magabtanka,
Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.
3 Sa’ad da na duba sararin sama, wanda ka yi,
Da wata da taurari waɗanda ka sa a wuraren zamansu,
4 Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi,
Mutum kurum, har da kake lura da shi?
5 Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi,
Ka naɗa shi da daraja da girma!
6 Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta,
Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa,
7 Tumaki da shanu, har ma da namomin jeji,
8 Da tsuntsaye da kifaye,
Da dukan halittar da suke cikin tekuna.
9 Ya Ubangiji, Ubangijinmu,
An san girmanka ko’ina a dukan duniya!