Elihu Ya Ɗaukaka Girman Allah
1 Elihu ya ci gaba da magana.
2 “Ka yi mini haƙuri kaɗan, ni kuwa zan nuna maka,
Gama har yanzu ina da abin da zan faɗa in kāre Allah.
3 Zan tattaro ilimina daga nesa,
In bayyana adalcin Mahaliccina.
4 Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba,
Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai.
5 “Ga shi kuwa, Allah Mai Girma, ba ya raina kowa,
Shi mai girma ne, mai cikakkiyar basira.
6 Ba ya rayar da masu laifi,
Amma yakan ba waɗanda ake tsananta wa halaliyarsu.
7 Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya,
Yakan kafa su har abada tare da sarakuna,
A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.
8 Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi,
Da kuma igiyar wahala,
9 Sa’an nan yakan sanar da su aikinsu
Da laifofin da suke yi na ganganci.
10 Yakan sa su saurari koyarwa,
Da umarnai, cewa su juya, su bar mugunta.
11 Idan suka kasa kunne suka bauta masa,
Za su cika kwanakinsu da wadata,
Shekarunsu kuma da jin daɗi.
12 Amma idan ba su kasa kunne ba,
Za a hallaka su da takobi,
Su mutu jahilai.
13 “Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu,
Suna tanada wa kansu fushi,
Ba su neman taimako sa’ad da ya ɗaure su.
14 Sukan yi mutuwar ƙuruciya,
Sukan ƙare kwanakinsu da kunya.
15 Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani,
Ta wurin tsananin da suke sha,
Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.
16 Allah ya tsamo ka daga cikin wahala,
Ya kawo ka yalwataccen wuri inda ba matsi,
Abincin da aka yi na addaras aka jera maka a kan tebur.
17 “Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye,
Amma hukunci da adalci sun kama ka.
18 Ka lura kada ka bar hasalarka ta sa ka raina Allah,
Kada kuma ka bar wahalar da kake sha ta sa ka ɓata da mai fansarka.
19 Kukanka ya iya raba ka da wahala,
Ko kuwa dukan ƙarfin da kake da shi?
20 Kada ka ƙosa dare ya yi,
Domin a lokacin nan ne mutane sukan watse,
Kowa ya kama gabansa.
21 Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta,
Gama saboda haka kake shan wannan tsanani,
Don a tsare ka daga aikata mugunta.
22 “Duba, Allah Maɗaukaki ne cikin ikonsa,
Wa ya iya koyarwa kamarsa?
23 Ba wanda zai iya tsara wa Allah abin da zai yi,
Wa ya isa ya ce masa ya yi kuskure?
24 “Ka tuna ka girmama aikinsa,
Wanda mutane suke yabo.
25 Dukan mutane sun ga ayyukansa,
Sun hango shi daga nesa.
26 Ga shi kuwa, Allah Maɗaukaki ne,
Ba mu kuwa san iyakar ɗaukakarsa ba,
Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
27 “Allah yakan sa ruwa ya zama tururi,
Ya maishe shi ruwan sama,
28 Wanda yakan kwararo daga sama,
Ya zubo wa ɗan adam a yalwace.
29 Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama,
Da tsawar da ake yi a cikinsu?
30 Ga shi, yakan baza waƙiya kewaye da shi,
Yakan rufe ƙwanƙolin duwatsu.
Zurfin teku yana nan da duhunsa.
31 Gama ta haka yakan shara’anta mutane,
Yakan ba da abinci a yalwace.
32 Ya cika hannunsa da walƙiya,
Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata.
33 Tsawarta tana nuna kasancewar Allah,
Ko shanu sun san da zuwan hadiri.”