Ayuba Ya Yi Kukan Matsayin da Yake Ciki
1 “Na gaji da rayuwa,
Ku ji ina fama da baƙin ciki.
2 Kada ka hukunta ni, ya Allah.
Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.
3 Daidai ne a gare ka ka yi mugunta?
Ka wulakanta abin da kai da kanka ka yi?
Sa’an nan ka yi murmushi saboda dabarun mugaye?
4 Yadda mutane suke duban abu, haka kake duba?
5 Kai ma ranka gajere ne kamar namu?
6 In haka ne, me ya sa kake bin diddigin dukan laifofina,
Kana farautar dukan abin da na yi?
7 Ka sani, ba ni da laifi,
Ka kuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.
8 “Da ikonka ne ka yi ni, ka siffata ni,
Yanzu kuma da ikon nan naka ne za ka hallaka ni.
9 Ka tuna, ya Allah, kai ka halicce ni, da yumɓu kuwa ka yi ni.
Za ka murtsuke ni ne, in kuma koma ƙura?
10 Kai ne ka ba mahaifina ƙarfin da zai haife ni,
Kai ne ka sa na yi girma a cikin cikin mahaifiyata.
11 Kai ne ka siffata jikina da ƙasusuwa da jijiyoyi,
Ka rufe ƙasusuwan da nama, naman kuma ka rufe da fata.
12 Kai ne ka ba ni rai da madawwamiyar ƙauna,
Kulawarka ce ta sa ni rayuwa.
13 Amma yanzu na sani,
Dukan lokacin nan kana da wani nufi a ɓoye game da ni.
14 Jira kake ka ga ko zan yi zunubi,
Don ka ƙi gafarta mini.
15 Da cewa na yi zunubi, na shiga uku ke nan a wurinka.
Amma sa’ad da na yi abin kirki ba na samun yabo.
Ina baƙin ciki ƙwarai, kunya ta rufe ni.
16 Da zan ci nasara a kan kowane abu,
Da sai ka yi ta farautata kamar zaki,
Kana aikata al’ajabai don ka cuce ni.
17 A koyaushe kakan karɓi shaida gāba da ni,
Fushinka sai gaba gaba yake yi a kaina,
Kakan yi mini farmaki a koyaushe.
18 “Ya Allah, me ya sa ka bari aka haife ni?
Da ma na mutu tun kafin wani ya gan ni!
19 Da a ce daga cikin cikin mahaifiyata an wuce da ni zuwa kabari
Da ya fi mini kyau bisa ga kasancewata.
20 Raina bai kusa ƙarewa ba? A bar ni kawai!
Bari in ci moriyar lokacin da ya rage mini.
21 An jima kaɗan zan tafi, ba kuwa zan komo ba faufau,
Zan tafi ƙasa mai duhu, inda ba haske,
22 Ƙasa mai duhu, da inuwoyi da ɗimuwa
Inda ko haske ma kansa duhu ne.”