Ayuba Ya Kai Kuka ga Allah
1 Ayuba ya yi magana ya la’anci ranar da aka haife shi.
2 Ya ce,
“Ya Ubangiji, ka la’anci ranan nan da aka haife ni.
3 Ka la’anci daren nan da aka yi cikina.
4 Ka mai da ranan nan ta zama duhu, ya Allah.
Kada a ƙara tunawa da wannan rana,
Kada haske ya ƙara haskakata.
5 Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin.
Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.
6 Ka shafe wannan dare daga cikin shekara,
Kada kuma a ƙara lasafta shi.
7 Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki.
8 Ka faɗa wa masu sihiri su la’anci wannan rana,
Su waɗanda suke umartar dodon ruwa.
9 Ka hana gamzaki haskakawa,
Kada ka bar daren nan ya sa zuciya ga wayewar gari,
10 Ka la’anci daren nan da aka haife ni,
Da ya jefa ni a baƙin ciki da wahala.
11 “Da ma na mutu tun a cikin cikin uwata,
Ko kuwa da haihuwata in mutu.
12 Me ma ya sa uwata ta rungume ni a ƙirjinta,
Ta shayar da ni kuma da mamanta?
13 Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce,
14 Da ina ta barcina kamar sarakuna da masu mulki
Waɗanda suka sāke gina fādodi na dā,
15 Da ina ta sharar barcina kamar shugabanni
Waɗanda suka cika gidajensu da zinariya da azurfa,
16 In yi ta sharar barci kamar jariran da aka haifa matattu.
17 Mugaye za su daina muguntarsu a kabari,
Ma’aikatan da suka gaji da aiki su ma za su huta,
18 Har ‘yan sarƙa ma za su ji daɗin salama,
Su huta daga tsautawa da umarnai masu tsanani.
19 Kowa da kowa yana wurin, babba da ƙarami duk ɗaya ne,
Bayi ma sun sami ‘yanci.
20 “Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa?
Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki?
21 Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa,
Sun fi son kabari da kowace irin dukiya.
22 Ba su da farin ciki, sai sun mutu an binne su tukuna.
23 Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba,
Ya kalmashe su kowane gefe.
24 A maimakon cin abinci, sai baƙin ciki nake yi,
Ba kuma zan daina yin nishi ba,
25 Dukan abin da nake jin tsoro ko fargaba ya faru.
26 Ba ni da salama, ba ni da hutawa,
Wahala ba za ta taɓa ƙarewa ba.”