Shaiɗan Ya Sāke Jarraba Ayuba
1 Sa’ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta sāke yi, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su.
2 Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ina ka fito?”
Sai Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, ko’ina a duniya.”
3 Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta. Kai ka sa na yardar maka ka far masa, ba tare da wani dalili ba. Amma duk da haka Ayuba yana nan da amincinsa kamar yadda yake.”
4 Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Mutum ya iya rabuwa da dukan abin da yake da shi don yă ceci ransa.
5 Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai yă fito fili yă zage ka.”
6 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Shi ke nan, yana cikin ikonka, amma fa, kada ka kashe shi.”
7 Sa’an nan Shaiɗan ya rabu da Ubangiji, ya je ya sa ƙuraje su fito ko’ina a jikin Ayuba.
8 Ayuba ya je ya zauna kusa da juji ya ɗauki tsingaro ya yi ta sosa ƙurajen.
9 Sai matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana da amincin nan naka? Don me ba za ka zagi Allah ka mutu ba?”
10 Ayuba ya amsa, ya ce mata, “Wace irin maganar gāɓanci ce haka? Lokacin da Allah ya aiko mana da alheri, mukan yi na’am da shi, to, me zai sa sa’ad da ya aiko mana da wahala za mu yi gunaguni?” Cikin dukan wahalar da Ayuba ya sha, bai sa wa Allah laifi ba.
Abokan Ayuba Sun Zo
11 Sa’ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na’ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta’azantar da shi.
12 Suka hango Ayuba tun daga nesa, amma ba su gane shi ba. Da suka gane shi sai suka fara kuka da murya mai ƙarfi. Suka kyakkece tufafinsu saboda baƙin ciki, suka ɗibi ƙura suka watsa a kawunansu.
13 Sa’an nan suka zauna a ƙasa tare da shi, har kwana bakwai, amma ba wanda ya ce uffan, saboda ganin irin yawan wahalar da yake sha.