ESTA 8

An Ba Yahudawa Izini Kada Su Miƙa Wuya

1 A wannan rana sai sarki Ahasurus ya ba Esta gidan Haman, maƙiyin Yahudawa, da duk dukiyar Haman. Mordekai kuwa ya zo gaban sarki, gama Esta ta bayyana yadda yake a gare ta.

2 Sa’an nan sarki ya ɗauki zobensa na hatimi, wanda ya karɓe a wurin Haman, ya ba Mordekai. Esta kuma ta ba Mordekai gidan Haman.

3 Sa’an nan kuma Esta ta faɗi a wajen ƙafafun sarki, ta roƙe shi da hawaye ya kawar da mugun shirin da Haman Ba’agage ya shirya wa Yahudawa.

4 Sai sarki ya miƙo wa Esta sandan sarauta na zinariya.

5 Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, “Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba’agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da suke cikin dukan lardunan sarki.

6 Gama ƙaƙa zan iya daurewa da ganin masifa da hallaka na mutanena da dangina?”

7 Sai sarki Ahasurus ya ce wa sarauniya da Mordekai, Bayahude, “Ga shi, na riga na ba Esta gidan Haman, an kuma riga an rataye shi a bisa gungume domin ya so ya taɓa Yahudawa.

8 Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba.”

9 A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.

10 An yi rubutu da sunan sarki Ahasurus, aka kuma hatimce shi da hatimin zoben sarki. Aka aika da wasiƙun ta hannun ‘yan-kada-ta-kwana, waɗanda suka hau dawakai masu zafin gudu da akan mora a aikin sarki.

11 A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da ‘ya’yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.

12 Za a yi wannan a dukan lardunan sarki Ahasurus ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar.

13 Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, Yahudawa kuwa su yi shiri saboda wannan rana, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.

14 Sai ‘yan-kada-ta-kwana suka hau dawakai masu zafin gudu waɗanda akan mora a aikin sarki, suka tafi da gaggawa don su iyar da dokar sarki. Aka yi shelar dokar a Shushan, masarauta.

15 Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu launin shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai launin shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shushan.

16 Yahudawa suka sami haske, da farin ciki, da murna, da daraja.

17 A kowane lardi da birni inda maganar sarki da dokarsa suka kai, Yahudawa suka yi farin ciki da murna, suka yi biki, suka yi hutu. Mutane da yawa daga cikin mutanen ƙasar suka zama Yahudawa, gama tsoron Yahudawa ya kama su.