Zaman da Ya Dace a Gaban Allah
1 Daga ƙarshe kuma ‘yan’uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,
2 domin kun san umarnin nan da muka yi muku da iznin Ubangiji Yesu.
3 Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,
4 kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,
5 ba ta muguwar sha’awa ba, yadda al’ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.
6 A cikin wannan al’amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan’uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.
7 Ai, ba a zaman ƙazanta ne Allah ya kira mu ba, amma ga zaman tsarki ne.
8 Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
9 A game da ƙaunar ‘yan’uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.
10 Hakika kuwa kuna ƙaunar dukan ‘yan’uwa a duk ƙasar Makidoniya. Sai dai muna muku gargaɗi, ‘yan’uwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,
11 kuna himmantuwa ga zaman lafiya, kuna kula da sha’anin gabanku kawai, kuna kuma aiki da hannunku, kamar yadda muka umarce ku,
12 domin ku zama masu mutunci ga waɗanda ba masu bi ba, kada kuma ku rataya a jikin kowa.
Matattu da Waɗanda Suke a Raye a Zuwan Ubangiji
13 Amma ‘yan’uwa, ba mu so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙin ciki kamar yadda sauran suke yi, marasa bege.
14 Tun da muka gaskata Yesu ya mutu, ya kuwa tashi, haka kuma albarkacin Yesu, Allah zai kawo waɗanda suka yi barci su zo tare da shi.
15 Muna kuwa shaida muku bisa ga faɗar Ubangiji, cewa mu da muka wanzu, muke kuma a raye har ya zuwa komowar Ubangiji ko kaɗan ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba,
16 domin Ubangiji kansa ma zai sauko daga Sama, da kira mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika, da kuma busar ƙahon Allah. Waɗanda suka mutu suna na Almasihu, su ne za fara tashi,
17 sa’an nan sai mu da muka wanzu, muke a raye, za a ɗauke mu tare da su ta cikin gajimare, mu sadu da Ubangiji a sararin sama, sai kuma kullum mu kasance tare da Ubangiji.
18 Saboda haka, sai ku yi wa juna ta’aziyya da wannan magana.