Maƙaƙashiyar Haman don Ya Hallaka Yahudawa
1 Bayan waɗannan abubuwa, sai sarki Ahasurus ya gabatar da Haman ɗan Hammedata Ba’agage. Ya fīfita shi bisa dukan sarakunan da suke tare da shi.
2 Dukan barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka rusuna suka yi wa Haman mubaya’a, gama sarki ya umarta a yi masa haka. Amma Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya’a ba.
3 Sai barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka ce wa Mordekai, “Me ya sa ka karya dokar sarki?”
4 Sa’ad da suka yi ta yi masa magana kowace rana, shi kuwa bai kasa kunne gare su ba, sai suka faɗa wa Haman, don su gani ko maganar Mordekai za ta tabbata, gama ya faɗa musu shi Bayahude ne.
5 Sa’ad da Haman ya ga Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya’a ba, sai ya husata.
6 Har ma ya ga a kashe Mordekai kaɗai, wannan bai isa ba. Da yake an faɗa masa asalin Mordekai, sai ya nema ya hallaka dukan Yahudawa, wato kabilar Mordekai, waɗanda suke a dukan mulkin Ahasurus.
7 A watan fari, wato watan Nisan, a shekara ta goma sha biyu ta sarautar sarki Ahasurus, sai suka yi ta jefa Fur, wato kuri’a, a gaban Haman kowace rana da kowane wata har kuri’a ta faɗo a kan watan goma sha biyu, wato watan Adar.
8 Sa’an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, “Akwai waɗansu mutane da suke warwatse a jama’ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su.
9 Idan ya gamshi sarki, bari a yi doka a hallaka su, ni kuwa zan ba waɗanda suke tafiyar da aikin sarki, talanti dubu goma (10,000) na azurfa, don su sa a baitulmalin sarki.”
10 Sarki kuwa ya zare zobensa na hatimi daga hannunsa ya ba Haman Ba’agage, ɗan Hammedata, maƙiyin Yahudawa.
11 Sa’an nan ya ce masa, “Da kuɗin, da mutanen duk an ba ka, ka yi yadda ka ga dama da su.”
12 Sai aka kirawo magatakardun sarki a rana ta goma sha uku ga watan fari. Bisa ga umarnin Haman aka rubuta doka zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da masu mulkin dukan larduna, da sarakunan shugabannin jama’a. Aka rubuta zuwa kowane lardi da irin rubutunsa, da kowaɗanne mutane kuma da harshensu da sunan sarki Ahasurus. Aka hatimce ta da hatimin zoben sarki.
13 Aka ba ‘yankada-ta-kwana takardun zuwa dukan lardunan sarki don a hallaka Yahudawa, a karkashe, a ƙarasa su, ƙanana da manya, mata da maza, duk a rana ɗaya, wato ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar, a kuma washe dukiyoyinsu.
14 Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, su kasance a shirye don ranar.
15 Bisa ga umarnin sarki, sai ‘yankada-ta-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a Shushan, masarauta. Sarki da Haman kuwa suka zauna don su sha, amma birnin Shushan ya ruɗe.