ESTA 1

Sarauniya Bashti Ta Raina Sarki Ahasurus

1 Ahasurus ya yi sarauta daga Hindu har zuwa Habasha, ya mallaki larduna ɗari da ashirin da bakwai.

2 A waɗannan kwanaki, sarki Ahasurus yake zaune a gadon sarautarsa a Shushan, masarauta.

3 A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya yi biki saboda sarakunansa, da barorinsa, da sarakuna yaƙin Farisa da Mediya, da manyan mutane, da hakiman larduna.

4 Sai ya nuna wadatar mulkinsa, da martabarsa, da darajarsa har kwanaki masu yawa, wato kwana ɗari da tamanin.

5 Bayan da waɗannan kwanaki sun cika, sai sarki ya yi wa manya da ƙanana waɗanda suke a Shushan, wato masarauta, biki, har na kwana bakwai a filin lambun fādar sarki.

6 Aka kewaye wurin da fararen labule da na shunayya na lallausan lilin, aka ɗaure da kirtani na lallausan lilin mai launin shunayya haɗe da zobban azurfa da ginshiƙai na sassaƙaƙƙun duwatsu masu daraja. Akwai gadaje na zinariya da na azurfa a kan daɓen da aka yi da duwatsu masu daraja, masu launi iri iri.

7 Aka ba da sha a finjalai iri iri na zinariya. Aka shayar da su da ruwan inabi irin na sarauta a yalwace bisa ga wadatar sarki.

8 Aka yi ta sha bisa ga doka, ba wanda aka matsa masa, gama sarki ya umarci fādawansa su yi wa kowa yadda yake so.

9 Sarauniya Bashti kuma ta yi wa mata babban biki a fādar sarki Ahasurus.

10 A rana ta bakwai sa’ad da zuciyar sarki take murna saboda ruwan inabi, sai ya umarta bābāninsa guda bakwai, waɗanda suke yi masa hidima, wato Mehuman, da Bizta, da Harbona, da Bigta, da Abagta, da Zetar, da Karkas,

11 su kirawo sarauniya Bashti ta zo wurinsa da kambin sarauta, don ya nuna wa jama’a da shugabanni kyanta, gama ita kyakkyawa ce.

12 Amma sarauniya Bashti ta ƙi zuwa kamar yadda sarki ya umarci bābānin su faɗa mata. Wannan ya sa sarki ya husata ƙwarai.

13 Sarki kuwa ya nemi shawara ga masu hikima waɗanda suka ƙware zamani, gama sarki ya saba da yin haka ga waɗanda suka san doka da shari’a.

14 Su ne mutanen da suke kusa da shi, wato Karshena, da Shetar, da Admata, da Tarshish, da Meres, da Marsena, da Memukan. Su ne sarakuna bakwai na Farisa da Mediya, su ne masu zuwa wurin sarki, su ne kuma na fari a mulkin.

15 Sarki ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi da sarauniya Bashti da yake ba ta yi biyayya da umarnin da na aika ta hannun babani ba?”

16 Sai Memukan ya amsa a gaban sarki da sauran sarakai, ya ce, “Ba sarki ne kaɗai sarauniya Bashti ta yi wa laifi ba, amma har dukan sarakai, da sauran jama’a da suke cikin dukan lardunan sarki Ahasurus.

17 Gama za a sanar wa dukan mata abin da sarauniya ta yi, gama abin da ta yi zai sa su raina mazansu, gama za su ce, ‘Sarki Ahasurus ya umarta a kirawo masa sarauniya Bashti, amma ta ki.’

18 Yau ma matan Farisa da Mediya waɗanda suka ji abin da sarauniya ta yi, haka za su faɗa wa dukan hakimai. Wannan zai kawo raini da fushi mai yawa.

19 Idan sarki ya yarda, bari ya yi doka, a kuma rubuta ta cikin dokokin Farisa da Mediya don kada a sāke ta, cewa Bashti ba za ta ƙara zuwa wurin sarki Ahasurus ba. Bari sarki ya ba da matsayinta na sarauta ga wata wadda ta fi ta.

20 Sa’ad da aka ji dokar sarki, wadda zai yi a dukan babbar ƙasarsa, dukan mata za su girmama mazansu, ƙanana da manya.”

21 Wannan shawara ta gamshi sarki da sauran sarakai, sarki ya yi kamar yadda Memukan ya shawarta.

22 Sai ya aika da takardu zuwa dukan lardunan sarki, kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da harshensu, domin kowane namiji ya zama shugaban gidansa, ya kuma zama mai faɗa a ji.