NEH 9

Jama’a Sun Hurta Laifofinsu

1 A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, sai jama’ar Isra’ila suka taru, suna azumi, suna saye da tufafin makoki, suna zuba toka a kansu.

2 Suka ware kansu daga bāre duka, suka tsaya, suna hurta laifofinsu da na kakanninsu.

3 Sa’ad da suke tsaye a inda suke, sai suka ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu na yini, suna karanta littafin dokokin Ubangiji Allahnsu. Suka kuma ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu ɗin na yinin, suna ta hurta laifofi suna kuma yi wa Ubangiji Allahnsu sujada.

4 Sai Yeshuwa, da Bani, da Kadmiyel, da Shebaniya, da Bunni, da Sherebiya, da Bani, da Kenani suka tsaya a kan dakalin Lawiyawa, suka ta da murya da ƙarfi ga Ubangiji Allahnsu.

5 Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce,

“Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku,

Ku yabe shi har abada abadin.

Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii,

Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”

Addu’ar Hurta Laifi

6 Sa’an nan suka yi wannan addu’a, suka ce,

“Kai kaɗai ne Ubangiji, ya Ubangiji,

Kai ne ka yi samaniya da taurari da sararin sama.

Kai ne ka yi ƙasa, da teku, da kowane abu da yake cikinsu,

Ka ba dukansu rai,

Ikokin samaniya sun rusuna suna maka sujada.

7 Kai ne, ya Ubangiji Allah, ka zaɓi Abram,

Ka fito da shi daga Ur ta Kaldiyawa,

Ka sāke sunansa ya zama Ibrahim.

8 Ka iske shi amintacce a gare ka,

Ka kuwa yi masa alkawari.

Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan’ana,

Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa,

Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa,

Ta zama inda zuriyarsa za su zauna.

Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.

9 Ka ga wahalar kakanninmu a Masar,

Ka ji kukansu a Bahar Maliya.

10 Ka kuma aikata alamu da al’ajabai a kan Fir’auna,

Da fadawansa duka, da mutanen ƙasarsa,

Gama ka san yadda suka yi wa jama’arka danniya.

Ta haka ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.

11 Ka yi hanya ta cikin teku domin jama’arka,

Ka sa su bi ta ciki a kan sandararriyar ƙasa.

Ka sa waɗanda suke fafararsu suka hallaka cikin zurfin teku,

Suka nutse kamar dutse.

12 Da rana ka bishe su da al’amudin girgije,

Da dare ka bishe su da al’amudin wuta.

13 Ka kuma sauka a bisa Dutsen Sinai,

Ka yi magana da jama’arka a can,

Ka ba su ka’idodin da suka dace,

Da dokoki, da kyakkyawar koyarwa.

14 Ka koya musu su kiyaye Asabar ɗinka tsattsarka,

Ka kuma ba su dokokinka ta hannun Musa bawanka.

15 Ka ba su abinci daga sama sa’ad da suka ji yunwa,

Ruwa kuma daga dutse sa’ad da suka ji ƙishi,

Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.

16 Amma kakanninmu suka yi fāriya, suka taurare,

Suka ƙi yin biyayya da umarnanka.

17 Suka ƙi yin biyayya,

Suka manta da dukan abin da ka yi,

Suka manta da al’ajaban da ka aikata.

Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba,

Don su koma cikin bauta a Masar.

Amma kai Allah ne mai gafartawa,

Kai mai alheri ne, mai ƙauna,

Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.

18 Ko sa’ad da suka yi wa kansu ɗan marakin zubi,

Suka ce shi ne allahn da ya fisshe su daga Masar,

Ai, sun yi maka ɓatanci, ya Ubangiji.

19 Amma ba ka rabu da su a hamada ba,

Saboda jinƙanka mai girma ne.

Ba ka kuwa kawar da girgije da wuta ba,

Waɗanda suke nuna musu hanya dare da rana.

20 Ta wurin alherinka ka faɗa musu abin da ya kamata su yi,

Ka ciyar da su da manna, ka ba su ruwa su sha.

21 Ka taimake su a jeji shekara arba’in,

Ka ba su dukan abin da suke bukata,

Ƙafafunsu ba su kumbura su yi musu ciwo ba.

22 “Ka sa sun ci al’ummai da mulkoki da yaƙi,

Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu.

Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon,

Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.

23 Ka riɓaɓɓanya zuriyarsu kamar taurarin sararin sama,

Ka sa suka ci ƙasar, suka zauna cikinta,

Ƙasar da aka yi wa kakanninsu alkawari za ka ba su.

24 Saboda haka zuriyarsu suka shiga, suka mallaki ƙasar Kan’ana.

Ka rinjayi mutanen da suke zama a can.

Ka ba jama’arka iko su yi yadda suke so

Da mutane, da sarakunan ƙasar Kan’ana.

25 Sun ci birane masu garu, da ƙasa mai dausayi,

Da gidaje cike da dukiya, da rijiyoyi, da gonakin inabi,

Da itatuwan zaitun, da itatuwa masu ‘ya’ya.

Suka ci dukan abin da suke so, suka yi taiɓa,

Suka mori dukan kyawawan abubuwan da ka ba su.

26 “Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka,

Suka juya wa dokokinka baya,

Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su,

Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka.

Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.

27 Saboda haka ka bar abokan gābansu su ci su, mallake su.

A wahalarsu sun yi kira gare ka domin taimako,

Ka kuwa amsa musu daga Sama.

Ta wurin jinƙanka mai yawa ka aiko musu da shugabanni,

Waɗanda suka kuɓutar da su daga maƙiyansu.

28 Sa’ad da zaman salama ya komo, sai kuma su yi zunubi,

Kai kuma sai ka bar abokan gabansu su ci su.

Duk da haka idan sun tuba, suka roƙe ka ka cece su,

Kakan ji daga Sama,sau da yawa,

Ka cece su da jinƙanka mai yawa.

29 Ka gargaɗe su su yi biyayya da koyarwarka,

Amma sun bijire wa dokoki saboda girmankai,

Ko da yake kiyaye dokarka ita ce hanyar rai.

Masu taurinkai sun taurare, sun ƙi yin biyayya.

30 “Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su,

Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne.

Saboda haka ka sa waɗansu al’ummai su mallaki jama’arka.

31 Duk da haka, saboda yawan jinƙanka,

Ba ka yashe su ko ka hallaka su ba.

Kai Allah mai alheri ne mai jinƙai!

32 “Ya Allah, Allahnmu, da girma kake!

Kai mai banrazana ne, cike da iko!

Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta.

Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu,

Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba!

Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu,

Da annabawanmu, da kakanninmu,

Da dukan sauran jama’arka sun sha wahala.

Ka san irin wahalar da muka sha.

33 Ka yi daidai da ka hukunta mu haka!

Kai mai aminci ne, mu kuwa mun yi zunubi.

34 Gama kakanninmu, da sarakunanmu,

Da shugabanninmu, da firistocinmu,

Ba su kiyaye dokarka ba.

Ba su kasakunne ga umarnanka da gargaɗinka ba.

Da waɗannan ne kake zarginsu.

35 Da albarkacinka sarakuna suke mulkin jama’arka,

Sa’ad da suke ƙasashen waje, ƙasa mai dausayi ka ba su,

Amma ba su juyo su bar zunubi, su bauta maka ba.

36 Ga shi, a yau mu bayi ne a ƙasar da ka ba mu,

Wannan ƙasa mai dausayi wadda take ba mu abinci.

37 Amfanin ƙasa duk yana tafiya ga sarakunan

Da ka ɗora su a kanmu saboda mun yi zunubi.

Suna yi mana yadda suka ga dama, mu da dabbobinmu,

Muna cikin baƙin ciki.”

Jama’a Sun Sa Hannu a Yarjejeniya

38 “Saboda wannan duka muke yin alkawari mai ƙarfi a rubuce. Shugabanninmu kuwa, da Lawiyawanmu, da firistocinmu, suka buga hatimi, suka sa hannu.”