Nehemiya Ya Zaɓi Masarautan Urushalima
1 Sa’ad da aka gina garun, aka sa ƙofofinsa, aka kuma sa matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da Lawiyawa,
2 sai na ba ɗan’uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.
3 Sa’an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje.
Lissafin Mutane
4 Birnin yana da faɗi da girma, amma mutanen da suke ciki kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje ba tukuna.
5 Allahna kuwa ya sa a zuciyata in tara manya da shugabanni, da sauran jama’a don a rubuta su bisa ga asalinsu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara komowa. Ga abin da na tarar aka rubuta ciki.
6 Waɗannan su ne mutanen lardin Yahuza, waɗanda suka komo daga zaman talala da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kai mutane. Sun komo Urushalima da Yahuza. Kowa ya tafi garinsu.
7 Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seraiya, da Re’elaya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana.
8-25 Ga jerin iyalan Isra’ila da adadin waɗanda suka komo daga zaman dole
iyalin Farosh, dubu biyu da ɗari da saba’in da biyu (2,172)
iyalin Shefatiya, ɗari uku da saba’in da biyu
iyalin Ara, ɗari shida da hamsin da biyu
iyalin Fahat-mowab, wato zuriyar Yeshuwa da Yowab, dubu biyu da ɗari takwas da goma sha takwas (2,818)
iyalin Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)
iyalin Zattu, ɗari takwas da arba’in da biyar
iyalin Zakkai, ɗari bakwai da sittin
iyalin Bani, ɗari shida da arba’in da takwas
iyalin Bebai, ɗari shida da ashirin da takwas
iyalin Azgad, dubu biyu da ɗari uku da ashirin da biyu (2,322)
iyalin Adonikam, ɗari shida da sittin da bakwai
iyalin Bigwai, dubu biyu da sittin da bakwai (2,067)
iyalin Adin, ɗari shida da hamsin da biyar
iyalin Ater (na Hezekiya), tasa’in da takwas
iyalin Hashum, ɗari uku da ashirin da takwas
iyalin Bezai, ɗari uku da ashirin da huɗu
iyalin Yora, ɗari da goma sha biyu
iyalin Gibeyon, tasa’in da biyar
26-38 Mutanen da kakanninsu suka zauna a waɗannan garuruwa, su ma sun komo daga zaman talala.
Baitalami da Netofa, ɗari da tamanin da takwas
Anatot, ɗari da ashirin da takwas
Azmawet, arba’in da biyu
Kiriyat-yeyarim da Kefira, da Biyerot, ɗari bakwai da arba’in da uku
Rama da Geba, ɗari shida da ashirin da ɗaya
Mikmash, ɗari da ashirin da biyu
Betel da Ai, ɗari da ashirin da uku
Da wani Nebo, hamsin da biyu
Da wani Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)
Harim, ɗari uku da ashirin
Yariko, ɗari uku da arba’in da biyar
Lod, da Hadid, da Ono, ɗari bakwai da ashirin da ɗaya
Senaya, dubu uku da ɗari tara da talatin (3,930)
39-42 Ga lissafin iyalin firistoci da suka komo daga zaman talala.
Yedaiya, na zuriyar Yeshuwa, ɗari tara da saba’in da uku
Immer, dubu ɗaya da hamsin da biyu (1,052)
Fashur, dubu da ɗari biyu da arba’in da bakwai (1,247)
Harim, dubu ɗaya da goma sha bakwai (1,017)
43 Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba’in da huɗu.
44 Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba’in da takwas.
45 Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.
46-56 Ma’aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su ne
Zuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,
Keros, da Siyaha, da Fadon,
Lebana, da Hagaba, da Shamlai,
Hanan, da Giddel, da Gahar,
Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,
Gazam, da Uzza, da Faseya,
Besai, da Me’uniyawa, da Nefushiyawa,
Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,
Bazlut, da Mehida, da Harsha,
Barkos, da Sisera, da Tema,
Neziya, da Hatifa.
57-59 Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su ne
na Sotai, da Hassoferet, da Feruda,
Yawala, da Darkon, da Giddel,
Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.
60 Jimillar zuriyar ma’aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa’in da biyu ne.
61-62 Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra’ilawa ba, su ɗari shida ne da arba’in da biyu.
63 Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri ‘yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa.
64 Waɗannan suka nema a rubuta su tare da waɗanda aka rubuta jerin sunayen asalinsu, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.
65 Sai mai mulki ya faɗa musu kada su ci abinci mafi tsarki, sai an sami firist wanda zai yi tambaya ta wurin Urim da Tummin tukuna.
66-69 Jimillar waɗanda suka komo duka su dubu arba’in da dubu biyu da ɗari uku da sittin ne (42,360)
barorinsu mata da maza, waɗanda yawansu ya kai dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337)
mawaƙa ɗari biyu da arba’in da biyar mata da maza
dawakansu kuma ɗari bakwai da talatin da shida ne
alfadaransu kuma ɗari biyu da arba’in da biyar ne
raƙumansu ɗari huɗu da talatin da biyar ne
jakunansu dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720)
70-72 Da yawa daga cikin jama’a suka ba da taimako domin biyan aikin gyaran Haikali.
Mai mulki ya ba da
zinariya darik dubu (1,000)
kwanonin wanke hannu guda hamsin
rigunan firistoci ɗari biyar da talatin
Shugabannin iyali suka ba da
zinariya darik dubu ashirin (20,000)
azurfa maina dubu biyu da ɗari biyu (2,200)
Sauran jama’a suka ba da
zinariya darik dubu ashirin (20,000)
azurfa maina dubu biyu (2,000)
rigunan firistoci guda sittin da bakwai
73 Sa’an nan firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron Haikali, da mawaƙa da waɗansu da dama daga cikin jama’a, da ma’aikatan Haikali, da dukan Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.