NEH 2

An Aika da Nehemiya Ya Tafi Urushalima

1 Ni kuwa ina riƙe da finjalin sarki. Wata rana a watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar sarki Artashate, sa’ad da na kai masa ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin, na ba shi. Ni ban taɓa ɓata fuskata a gabansa a dā ba, sai wannan karo.

2 Sai sarki ya tambaye ni, ya ce, “Me ya sa fuskarka ta ɓaci, ga shi, ba ciwo kake yi ba. Ba abin da ya kawo wannan, sai lalle kana baƙin ciki.”

Sai na tsorata ƙwarai,

3 na ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, me zai hana fuskata ta ɓaci, da yake birni inda makabartar kakannina take ya zama kango, an kuma ƙone ƙofofinsa da wuta?”

4 Sa’an nan sarki ya ce mini, “To, me kake so?”

Sai na yi addu’a ga Allah na Sama,

5 sa’an nan na ce wa sarki, “Idan ka yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, ka yardar mini in tafi Yahuza, birnin kakannina, inda makabartarsu take domin in sāke gina shi.”

6 Sarki kuwa, a sa’an nan sarauniya tana zaune kusa da shi, ya ce mini, “Kwana nawa za ka yi, yaushe kuma za ka dawo?” Sai na faɗa masa, ya kuwa yardar mini in tafi, ni kuwa na yanka masa kwanakin da zan yi.

7 Sa’an nan na ce wa sarki, “Idan sarki ya yarda, sai a ba ni takarda zuwa ga masu mulki da suke a lardin Yammacin Kogin Yufiretis domin su yardar mini in wuce zuwa Yahuza.

8 A kuma ba ni takarda zuwa ga Asaf, sarkin daji, domin ya ba ni katakan da zan yi jigajigan ƙofofin kagarar Haikali, da na garun birnin, da na gidan da zan zauna.” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.

9 Da na zo wurin masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis, sai na miƙa musu takardar sarki. Sarki ya haɗa ni da sarkin yaƙi da mahayan dawakai.

10 Amma Sanballat Bahorone, da Tobiya, Ba’ammone, bawa, ba su ji daɗi ba ko kaɗan sa’ad da suka ji labari, cewa wani ya zo domin ya inganta zaman lafiyar mutanen Isra’ila.

Nehemiya Ya Ƙarfafa Maginan Garu

11 Da na iso Urushalima na yi kwana uku,

12 sai na fita da dare tare da waɗansu mutane kima,ban faɗa wa kowa abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi wa Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.

13 Da na fita, sai na bi ta Ƙofar Kwari zuwa Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, na dudduba garun Urushalima, wanda aka rushe, da ƙofofinsa da wuta ta cinye.

14 Na yi gaba zuwa Ƙofar Maɓuɓɓuga da Tafkin Sarki, amma dabbar da na hau ba ta sami wurin wucewa ba.

15 Haka kuwa na fita da dare ta hanyar kwari na dudduba garun, sa’an nan na koma ta Ƙofar Kwari.

16 Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da na yi ba, gama ban riga na faɗa wa Yahudawa, da firistoci, da manyan gari, da shugabanni, da sauran waɗanda za su yi aikin ba.

17 Sa’an nan na ce musu, “Kun ga irin wahalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta. Ku zo, mu sāke gina garun Urushalima don mu fita kunya.”

18 Na kuma faɗa musu yadda Allah yana tare da ni, ya kuma taimake ni, da maganar da sarki ya faɗa mini.

Sai suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Suka himmatu su yi wannan aiki nagari.

19 Amma sa’ad da Sanballat Bahorone, da Tobiya Ba’ammone, bawa, da Geshem Balarabe, suka ji labari, sai suka yi mana ba’a, suka raina mu, suka ce, “Me kuke yi? Kuna yi wa sarki tayarwa ne?”

20 Ni kuwa sai na amsa musu, na ce, “Allah na Sama zai ba mu nasara, saboda haka mu mutanensa za mu tashe, mu kama gini, amma ba ruwanku, ba hakkinku, ba ku da wani abin tunawa a Urushalima.”