Sarki Yehowahaz na Yahuza
1 Jama’ar ƙasa kuwa suka ɗauki Yehowahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki. Ya gaji tsohonsa a Urushalima.
2 Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima wata uku.
3 Sai Sarkin Masar ya tuɓe shi daga sarautarsa ta Urushalima, ya sa su biya gandu, su ba da azurfa talanti ɗari, da zinariya talanti guda.
4 Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwansa, sarki a Yahuza da Urushalima. Ya sa masa sabon suna Yehoyakim. Amma Neko ya ɗauko Yehowahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai shi Masar.
Sarki Yehoyakim na Yahuza
5 Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa.
6 Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya ɗaure shi da sarƙoƙi, ya kai shi Babila.
7 Nebukadnezzar kuma ya kwaso waɗansu tasoshi da tukwane na Haikalin Ubangiji, ya kai Babila, ya ajiye su a fādar Babila.
8 Sauran ayyukan Yehoyakim da irin abubuwan da ya yi na banƙyama, da irin laifofinsa, suna nan, an rubuta su a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuza. Ɗansa Yekoniya kuwa ya gāji gadon sarautarsa.
An Kama Sarki Yekoniya
9 Yekoniya yana da shekara takwas sa’ad da ya ci sarauta, ya yi sarauta a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.
10 Da bazara sai sarki Nebukadnezzar ya aika aka kawo shi Babila tare da kayayyaki masu daraja na Haikalin Ubangiji. Ya kuma naɗa Zadakiya ɗan’uwan Yekoniya ya zama Sarkin Yahuza da Urushalima.
Sarki Zadakiya na Yahuza
11 Zadakiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta, ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarautar Urushalima.
12 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa. Bai nuna ladabi a gaban annabi Irmiya ba, wanda ya faɗa masa abin da Ubangiji ya ce.
Fāɗuwar Urushalima
13 Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra’ila.
14 Dukan manyan firistoci da sauran jama’a gaba ɗaya, sun zama marasa aminci ƙwarai suna aikata dukan abubuwan banƙyama da al’ummai suke yi. Suka ƙazantar da Haikalin Ubangiji wanda ya tsarkake a Urushalima.
15 Sai Ubangiji, Allah na kakanninsu, ya yi ta aika musu da manzanni saboda yana juyayin jama’arsa da wurin zaman zatinsa.
16 Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba’a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba’a, sai Ubangiji ya husata da jama’arsa don abin ya kai intaha.
An Kai Yahuza Bautar Talala
17 Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.
18 Ya kwaso dukan kayayyakin da suke a Haikalin Allah, manya da ƙanana, da dukiyar da take a Haikalin Allah, da ta sarki, da ta sarakunansa ya kai su Babila.
19 Suka ƙone Haikalin Allah suke rushe garun Urushalima, suka ƙone dukan fādodinta, suka lalatar da dukan kayanta masu daraja.
20 Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na ‘ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa,
21 don maganar ta cika wadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Irmiya, har lokacin da ƙasar take shan hutawar asabatanta na zamanta kango har shekara saba’in, ta kiyaye asabatai.
22 Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.
23 Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza. Duk wanda yake na mutanensa da suke nan, Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima.”