Assuriyawa sun Yi Barazana ga Urushalima
1 Bayan waɗannan abubuwa, da waɗannan ayyukan aminci, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa Yahuza yaƙi, ya kafa sansani kewaye da garuruwa masu garu, yana zaton zai ci su da yaƙi su zama nasa.
2 Da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo da nufin ya yi yaƙi da Urushalima,
3 sai ya yi shawara shi da jarumawansa da manyan mutanensa, su datse ruwan da yake fitowa daga maɓuɓɓugar da suke bayan birni, suka kuwa taimake shi.
4 Don haka mutane da yawa suka taru suka daddatse dukan maɓuɓɓugai da rafuffuka da suke gudu cikin ƙasar, suna cewa, “Bari mu hana sarakunan Assuriya samun ruwa idan sun iso Urushalima.”
5 Sai ya kama aiki gadangadan, ya sāke gina dukan garukan da suka rushe, ya gina hasumiya a kai, ya kuma gina wani garu bayan wannan, ya ƙara ƙarfin Millo a birnin Dawuda, ya kuma yi makamai na yaƙi da garkuwoyi masu yawan gaske.
6 Sai ya sa manyan sojoji su shugabanci jama’a. Su tattaro su gare shi a dandalin ƙofar birni, ya yi musu magana ta ƙarfafawa ya ce,
7 “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda Sarkin Assuriya, da dukan taron da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.
8 Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza.
9 Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa’an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa,
10 “Ga abin da Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya ce, ‘Ga me kake dogara, da har yanzu kuka dāge a cikin Urushalima, ga shi kuwa, yaƙi ya kewaye ta?
11 Ai, Hezekiya, ba ruɗinku yake yi ba, don ya sa ku mutu da yunwa da ƙishi sa’ad da yake ce muku Ubangiji Allahnku zai cece ku daga hannun Sarkin Assuriya?
12 Ashe, ba wannan Hezekiya ba ne ya ɗauke masujadansa da bagadansa, ya kuma umarci Yahuza da Urushalima, su yi sujada a gaban bagade guda, a kansa ne kuma za su ƙona hadayu?
13 Ashe, ba ku san abin da ni da kakannina muka yi wa dukan jama’ar waɗansu ƙasashe ba? Gumakan al’umman waɗannan ƙasashe sun iya ceton ƙasashensu daga hannuna?
14 Daga cikin dukan gumakan waɗannan al’ummai waɗanda kakannina suka hallakar da su sarai, ba wanda ya iya ceton jama’arsa daga hannuna, har da Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?
15 Yanzu fa kada ku yarda Hezekiya ya ruɗe ku, ko ya ɓad da ku haka, kada kuwa ku gaskata shi, gama ba wani gunki na wata al’umma, ko wani mulki wanda ya taɓa ceton jama’arsa daga hannuna, ko kuma daga hannun kakannina. Wane Allah naku har da zai iya cetonku daga hannuna?’ ”
16 Barorinsa kuwa suka ƙara yin maganganun saɓo gāba da Ubangiji Allah da bawansa Hezekiya.
17 Ya kuma rubuta wasiƙu, ya zargi Ubangiji Allah na Isra’ila, ya yi maganar saɓo, yana cewa, “Kamar yadda gumakan al’umman sauran ƙasashe suka kāsa ceton jama’arsu daga hannuna, haka nan kuma Allahn Hezekiya ba zai iya ceton jama’arsa daga hannuna ba.”
18 Da babbar murya, da Yahudanci kuwa, suka yi ta yin magana da jama’ar Urushalima waɗanda suke kan garu, don a tsoratar da su, a kuma firgita su, don su ci birnin.
19 Suka yi ta magana a kan Allah na Urushalima, kamar yadda suka yi magana a kan gumakan al’ummai, wato aikin hannuwan mutane.
Ubangiji Ya Ceci Hezekiya
20 Sai sarki Hezekiya, da annabi Ishaya ɗan Amoz, suka yi addu’a saboda wannan al’amari, suka yi kuka zuwa Sama.
21 Ubangiji kuwa ya aiki mala’ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa’ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin ‘ya’yan cikinsa suka kashe shi da takobi.
22 Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mazaunan Urushalima daga hannun Sennakerib Sarkin Assuriya, daga kuma hannun dukan maƙiyansa, ya hutar da su ta kowace fuska.
23 Mutane da yawa suka kawo wa Ubangiji sadakoki a Urushalima, suna kuma kawo wa Hezekiya Sarkin Yahuza abubuwa masu daraja. Saboda haka ya sami ɗaukaka a idon dukan sauran al’ummai, tun daga wannan lokaci har zuwa gaba.
Hezekiya Ya Yi Ciwo
24 A kwanakin nan kuwa Hezekiya ya yi ciwo gab da mutuwa, sai ya yi addu’a ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ya ba shi alama.
25 Amma Hezekiya bai nuna godiya a kan amfanin da ya samu ba, saboda girmankai. Saboda haka hasala ta auka kansa, da kan Yahuza da Urushalima.
26 Amma Hezekiya ya ƙasƙantar da kansa saboda girmankan da ya yi, shi da mazaunan Urushalima, saboda haka hasalar Ubangiji ba ta faɗa musu a kwanakin Hezekiya ba.
Hezekiya ya Karɓi ‘Yan Saƙo daga Babila
27 Hezekiya yana da dukiya ƙwarai, yana kuma da girma. Sai ya gina wa kansa taskoki inda zai ajiya azurfa, da zinariya, da duwatsu masu daraja, da kayan yaji, da garkuwoyi, da dukan tasoshi, da kwanoni masu daraja.
28 Yana kuma da ɗakunan ajiya na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai. Yana da wuraren turke shanu na kowane iri, yana kuma da garkunan tumaki.
29 Ya kuma giggina wa kansa birane, yana da garkunan tumaki da na awaki, da na shanu a yalwace. Gama Allah ya mallakar masa da abubuwa masu yawa.
30 Hezekiyan nan kuwa ya datse ruwan da yake gangarawa daga kogin Gihon, ya karkatar da su su gangara zuwa wajen yammacin birnin Dawuda. Hezekiya ya arzuta da dukan ayyukan da ya yi.
31 A kan ‘yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al’ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.
Mutuwar Hezekiya
32 Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, ga shi, an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a littafin sarakunan Yahuza da na Isra’ila.
33 Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin ‘ya’yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.