Yin Idin Ƙetarewa
1 Sai Hezekiya ya aika zuwa ga dukan Isra’ila da Yahuza, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa ga Ifraimu, da Manassa, cewa sai su zo Haikalin Ubangiji a Urushalima, domin su yi Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra’ila.
2 Gama sarki da sarakunansa da dukan majalisar da take a Urushalima sun tsai da shawara a yi Idin Ƙetarewa a wata na biyu,
3 gama ba su iya yinsa a lokacinsa ba, saboda yawan firistocin da suka tsarkake kansu bai isa ba, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.
4 A ganin sarki da na jama’a duka, shirin ya yi daidai.
5 Sai suka ba da umarni a yi shela a Isra’ila duka, tun daga Biyer-sheba, har zuwa Dan, cewa sai mutane su zo Idin Ƙetarewa na Ubangiji Allah na Isra’ila a Urushalima, gama jama’a mai yawan gaske ba su zo wurin yin idin kamar yadda aka umarta ba.
6 Sai mazanni suka tafi ko’ina da ina a dukan ƙasar Isra’ila da ta Yahuza da wasiƙu daga wurin sarki da sarakunansa, yadda sarki ya umarta.
“Ya ku jama’ar Isra’ila, ku komo wurin Ubangiji Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra’ila domin ya sāke juyowa zuwa ga sauranku, waɗanda kuka kuɓuta daga hannun sarakunan Assuriya.
7 Kada fa ku zama kamar kakanninku ko ‘yan’uwanku, marasa bangaskiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu, saboda haka ya maishe su kufai kamar yadda kuka gani.
8 Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.
9 Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, ‘yan’uwanku da ‘ya’yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”
10 Manzannin fa suka tafi gari gari a ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, har zuwa Zabaluna, amma suka yi musu dariyar raini, suka yi musu ba’a.
11 Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali’u, suka zo Urushalima.
12 Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.
13 Mutane da yawa kuwa suka zo Urushalima don su yi idin abinci marar yisti a wata na biyu, aka yi babban taro.
14 Sai suka kama aiki, suka kawar da bagadan da suke cikin Urushalima, da dukan bagadan ƙona turare suka kwashe suka zubar a kwarin Kidron.
15 Suka yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Suka sa firistoci da Lawiyawa su sha kunya, saboda haka sai suka tsarkake kansu, suka kawo hadayu na ƙonawa a Haikalin Ubangiji.
16 Sai suka ɗauki matsayinsu wanda aka ayyana bisa ga dokar Musa, mutumin Allah, firistocin suka yarfa jinin da suka karɓa daga hannun Lawiyawa.
17 Gama akwai waɗansu da yawa daga cikin taron waɗanda ba su tsarkake kansu ba, saboda haka ya zama tilas Lawiyawa su yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa saboda dukan wanda ba shi da tsarki, domin a tsarkake shi ga Ubangiji.
18 Gama akwai jama’a jingim, da yawa kuwa mutanen Ifraimu ne, da na Manassa, da na Issaka, da na Zabaluna, da ba su tsarkake kansu ba, duk da haka sun ci Idin Ƙetarewa ba yadda aka ƙayyade ba. Sai Hezekiya ya yi addu’a dominsu, yana cewa, “Ya Ubangiji mai alheri, ka gafarta wa ko wanne
19 wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko bai yi bisa kan dokar tsarkakewa na Wuri Mai Tsarki ba.”
20 Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya, ya warkar da jama’ar.
21 Jama’ar Isra’ila waɗanda suke a Urushalima kuwa sun yi idin abinci marar yisti da murna mai yawa, har kwana bakwai. Lawiyawa kuma da firistoci suka yabi Ubangiji kowace rana, suna raira waƙa da iyakar ƙarfinsu ga Ubangiji.
22 Hezekiya kuwa ya yi magana ta ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna fasaha a hidimar Ubangiji.
An Ƙara Yin Idin
Mutane fa suka ci abincin idin har kwana bakwai, suna miƙa hadayu na salama, suna ta yin godiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
23 Sai dukan taron suka yarda su ci gaba da yin idin har waɗansu kwana bakwai ɗin kuma, sai suka ci gaba da yin idin har kwana bakwai da murna.
24 Gama Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu bakwai (7,000), don yin hadayu, sarakuna kuma sun ba taron bijimai dubu (1,000) da tumaki dubu goma (10,000). Firistoci da yawa suka tsarkake kansu.
25 Dukan taron Yahuza, da firistoci, da Lawiyawa, da dukan taron jama’a da suka zo daga Isra’ila, da baƙi waɗanda suka zo daga ƙasar Isra’ila, da baƙin da suka zauna a Yahuza, suka yi murna.
26 Saboda haka an yi babban farin ciki a Urushalima, gama tun daga zamanin Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra’ila, ba a yi wani abu kamar haka a Urushalima ba.
27 Sai firistoci da Lawiyawa suka tashi suka sa wa jama’a albarka, aka kuwa ji muryarsu, addu’arsu kuma ta kai wurin zamansa a Sama.