Sarki Azariya na Yahuza
1 Dukan jama’ar Yahuza fa suka ɗauki Azariya, ɗan shekara goma sha shida, suka naɗa shi sarki, ya gāji gadon sarautar tsohonsa Amaziya.
2 Ya gina Elat, ya komar da ita ga Yahuza, bayan rasuwar sarki.
3 Azariya yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu, sunan tsohuwarsa Yekoliya ta Urushalima.
4 Azariya ya yi abin da yake daidai saboda Ubangiji, bisa ga dukan irin abin da tsohonsa Amaziya ya aikata.
5 Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.
6 Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.
7 Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa, da Larabawa, waɗanda suke zaune a Gur-ba’al, da kuma Me’uniyawa.
8 Ammonawa kuma suka kawo masa haraji, sunan Azariya ya kai har kan iyakar Masar, gama ya shahara ƙwarai.
9 Banda haka kuma, Azariya ya gina hasumiyai a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, da Ƙofar Kwari, da kan kusurwa, ya kuma yi musu kagara.
10 Ya kuma gina hasumiyai a jeji, ya haƙa tafukka masu yawa, saboda yana da garkunan dabbobi da yawa, da waɗanda suke Shefela da waɗanda suke a filin tudu. Yana kuma da manoma da masu yi wa kurangar inabi aski a tuddai, da wajen ƙasashe masu dausayi, gama shi mai son noma ne ƙwarai.
11 Har yanzu kuma, Azariya yana da rundunar sojoji waɗanda suka iya yaƙi ƙungiya ƙungiya, yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’aseya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin ‘yan majalisar sarki.
12 Jimillar shugabannin gidajen kakanni na ƙarfafan mutane jarumawa, dubu biyu da ɗari shida (2,600) ne.
13 Suna da sojoji dubu ɗari uku da dubu bakwai da ɗari biyar (307,500) a ƙarƙashin ikonsu waɗanda suke da ƙarfin yin yaƙi sosai, da za su taimaki sarki a kan maƙiyansa.
14 Azariya ya shirya wa sojojinsa garkuwoyi, da māsu, da kwalkwali, da sulke, da bakuna, da duwatsun majajjawa.
15 A Urushalima ya yi na’urori waɗanda gwanayen mutane ne suka ƙago don a sa su a hasumiya, da kan kusurwoyi, don a harba kibau, da manyan duwatsu. Da haka sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako mai banmamaki, har ya zama mai ƙarfin gaske.
An Hukunta Azariya Saboda Girmankai
16 Amma sa’ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.
17 Amma Azariya firist, ya bi shi tare da firistoci tamanin na Ubangiji, mutane ne jarumawa.
18 Sai suka hana sarki Azariya, suka ce masa, “Ba aikinka ba ne, Azariya, ka ƙona turare ga Ubangiji, wannan aikin firistoci ne, ‘ya’yan Haruna, waɗanda aka keɓe su don ƙona turare. Fita daga wurin nan mai tsarki, gama ka yi kuskure, ba za ka sami daraja daga wurin Ubangiji Allah ba.”
19 Azariya ya yi fushi, a lokacin kuwa yana riƙe da farantin ƙona turare a hannunsa, sa’ad da ya yi fushi da firistocin, sai kuturta ta faso a goshinsa, a nan gaban firistocin a cikin Haikalin Ubangiji, wajen bagaden ƙona turare.
20 Sai Azariya babban firist tare da sauran firistocin suka dube shi, sai ga kuturta a goshinsa! Sai suka tunkuɗa shi waje nan da nan. Shi kansa ma ya hazarta ya fita saboda Ubangiji ya buge shi.
21 Ta haka sarki Azariya ya kuturce, har zuwa ranar mutuwarsa. Saboda kuturtarsa, ya zauna a keɓe a wani gida, gama an fisshe shi daga Haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa shi ya shugabanci iyalin gidan sarki, yana kuma mulkin jama’ar ƙasa.
22 Sauran ayyukan Azariya, daga farko har zuwa ƙarshe, annabi Ishaya ɗan Amoz ya rubuta su.
23 Azariya ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a hurumin sarakuna, gama suka ce, “Shi kuturu ne.” Sai Yotam ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.