Sarki Asa na Yahuza
1 Sarki Abaija kuwa ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda. Ɗansa Asa shi ya gāji gadon sarautarsa. Ƙasar ta sami sakewa har shekara goma a zamaninsa.
2 Asa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.
3 Ya kawar da baƙin bagadai da masujadai, ya rurrushe ginshiƙai, ya kuma tumɓuke Ashtarot.
4 Ya umarci Yahuza su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kiyaye doka, da umarni.
5 Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagadan ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa.
6 Ya giggina birane masu kagara a Yahuza, gama ƙasar tana zaman lafiya. A waɗannan shekaru bai yi yaƙi da kowa ba, saboda Ubangiji ya kawo masa salama.
7 Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta.
8 Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, ‘yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.
9 Sai Zera mutumin Habasha ya zo da soja zambar dubu (1,000,000) da karusa ɗari uku har Maresha, don ya yi yaƙi da su.
10 Don haka sai Asa ya fito ya gamu da shi, suka kuwa jā dāga a kwarin Zefata a Maresha.
11 Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa’ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama’arka.”
12 Ubangiji kuwa ya fatattaki Habashawa a gaban Asa da Yahuza, Habashawa kuwa suka gudu.
13 Sai Asa da jama’ar da suke tare da shi, suka runtume su har zuwa Gerar. Habashawa suka fāɗi duka, ko ɗaya, ba wanda ya ragu da rai, gama an ragargaza su a gaban Ubangiji da gaban sojojin. Mutane suka kwashe ganima mai yawa gaske.
14 Suka hallaka dukan birane da suke kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka washe dukan biranen, gama biranen suna cike da ganima.
15 Suka kware alfarwan masu kiwon dabbobi, suka kora tumaki, da raƙuma masu yawan gaske. Sa’an nan suka komo Urushalima.